An tsinci gawar ɗan sanda, matarsa da ƴaƴansu 5 a cikin gidansu

An tsinci gawar ɗan sanda, matarsa da ƴaƴansu 5 a cikin gidansu

  • Wani jami'in dan sandan Nigeria da matarsa da yara biyar sun rasu a gidansu a Osun
  • Mutanen unguwa sun gano hakan ne bayan sun balle kofar gidan da safiyar Talata
  • Rundunar yan sandan jihar Osun ta tabbatar da afkuwar lamarin ta kuma fara bincike

Isokan, Jihar Osun - Wani abin bakin ciki ya faru a kauyen Elegbaata, Oke Suna, Apomu, karamar hukumar Isokan a jihar Osun bayan an tsinci gawar mutum bakwai - miji, mata da yaransu biyar - a cikin gidansu, The Punch ta ruwaito.

Sahara Reporters ta ruwaito cewa an ceto mutum daya daga iyalansu wanda shima ya kwana a gidan an garzaya da shi asibiti a Apomu, inda ake ba shi kulawa.

Wani mazaunin garin, da ya nemi a sakayya sunansa, ya ce mutum takwas ne suka kwana a gidan a ranar Litinin, amma an tsinci gawar bakwai da safen ranar Talata.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An Sake Kashe Mutum 7 a Jos Bayan Kisan Gillan da Akai Wa Musulmai

Yadda mutanen gari suka gano abin da ya faru?

Mazaunin ya ce mutanen unguwar sun damu ne bayan an lura cewa gari ya waye amma kofar gidan na rufe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An tsinci gawar dan sanda, matarsa da yayansa 5 a gidansu
Kwamishinan 'yan sandan jihar Osun, Olawale Olakode. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Majiyar ta kara da cewa:

"Duk da hakan, ba mu san cewa wadanda suka kwana a gidan sun mutu ba sai lokacin da wasu suka yi karfin hali suka balle kofar gidan.
"Abin da muka gani ya razana mu. dukkansu da suka kwana a gidan sun mutu illa mutum daya; miji, mata, yaransu biyar duk sun mutu. Amma an ceto mutum daya da ransa an kai shi asibiti. Wasu mutanen da suke nan lokacin da aka bude gidan sun ce sun shaki warin wani kemikal, amma ba zan iya tabbatarwa shine ya kashe su ba.
"Matar ce ke da gidan da abin ya faru. Mutumin da ya mutu a gidan mijinta ne, amma yaran ba nashi bane. Mutumin yana da gidansa a Apomu. Dan sanda ne mai suna Saheed."

Kara karanta wannan

Sunayen Matafiya fiye da 20 da aka yi wa kisan gilla a Jos, wani ya rasa 'yanuwansa 7

Rundunar yan sanda ta tabbatar da afkuwar lamarin

Kakakin yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola ta tabbatar da afkuwar lamarin.

Ta ce:

"An dauke gawar wadanda suka rasu an kai asibiti don gwaji. An kai su asibitin koyarwa na OAU, Ile-Ife. An fara bincike, duk da cewa ba a kama kowa ba.
"Mutumin da ake ceto yana samun kulawa a asibiti mai zaman kansa a Apomu; yana samun sauki."

An Kama Matar Ɗan Bindiga a Katsina Da N2.4m, Mijin Ya Tsere Ya Bar Ta

A wani labarin, yan sanda a jihar Katsina sun kama wata matar aure, Aisha Nura, mai shekaru 27 dauke da kudi Naira miliyan 2.4 na cinikin makamai da aka sayarwa yan bindiga, The Punch ta ruwaito.

An kama Aisha, da aka ce matar dan bindiga ne, a ranar 25 ga watan Yuli a yayin da ta ke shirin hawa kan babur din haya (acaba) daga Batsari zuwa kauyen Nahuta.

Kara karanta wannan

Kungiyar Kiristoci ta CAN ta fadi matsayarta kan kashe Muslulmai da aka yi a Jos

Mai magana da yawun yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da hakan a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: