An Tsinci Gawar Wani Jami'in Ɗan Sanda A Gidansa A Abuja

An Tsinci Gawar Wani Jami'in Ɗan Sanda A Gidansa A Abuja

  • An shiga juyayi da zaman makoki bayan gano gawar wani mataimakin sufritandan yan sanda, ASP, Salisu Garba Zuba a gidansa
  • Adamu Garba, dan uwan marigayin ya tabbatar da rasuwarsa yana mai cewa ya dawo daga aiki daren Alhamis ya kwanta
  • Garba ya ce an tafi dakin marigayin domin a tashe shi ya yi shirin zuwa sallar Juma'a amma aka gano ba ya numfashi aka garzaya da shi asibiti, likitoci suka tabbatar ya rasu

FCT, Abuja - An gano gawar wani jami'in dan sanda, mataimakin sufritanda, ASP, Salisu Garba Zuba a gidansa da ke unguwar Zuba, karamar hukumar Gwagwalada a Abuja a ranar Juma'a.

Dan uwan marigayin mai suna Adamu Garba, ya ce Zuba ya rasu ne ba da dadewa ba bayan ya dawo daga aiki a daren ranar Alhamis a ofishin yan sandan na Gwagwalada, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Jigon PDP Bode George Ya Lissafa Kasashen Da Zai Iya Yin Hijira Saboda Bola Tinubu Ya Zama Zababben Shugaban Kasa

Rundunar yan sanda
An Tsinci Gawar Wani Jami'in Ɗan Sanda A Gidansa A Abuja. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Yadda ASP Zuba ya rasu

Ya ce Zuba, wanda lafiyarsa kalau, ya dawo daga aiki kuma ya ce bari ya huta a dakinsa, amma aka gano ya rasu a lokacin da dan uwansa ya tafi ta tada shi don zuwa sallar Juma'a.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kara da cewa an garzaya da Zuba zuwa asibiti inda likita ya tabbatar cewa ya rasu, ya kuma ce tuni dai an yi wa marigayin jana'iza bisa koyarwar addinin musulunci.

City and Crime ta tattaro cewa marigayin dan sandan wanda ya rasu yana da shekaru 42, dan kabilar Koro daga Zuba, ya rasu ya bar matan aure biyu da yara guda bakwai.

An tsinci gawar wani dan kasuwa a dakin otel a jihar Bauchi

A wani rahoton na daban kun ji cewa an gano gawar wani Mista Chukwunonso Chukwujekwu a yankin Tudun Wada a garin Boi, da ke karamar hukumar Bogoro na jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

A shirye nake: Zababben gwamnan Katsina ya fadi abin da zai a ranar da ya karbi mulki

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, Chukwunonso mai rasuwa dan ainihin karamar hukumar Anambra ta gabas ne sai dai ya dade yana kasuwanci da zama a kauyen Boi a Bauchi.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Bauchi SP Ahmed Wakil ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya kara da cewa kwamishinan yan sandan Bauchi ya umurci a zurfafa bincike don gano sababin mutuwarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel