"Muna Lalata da Sama da Maza 12 a Rana": An Ji Ta Bakin 'Yan Mata da Ke Karuwanci

"Muna Lalata da Sama da Maza 12 a Rana": An Ji Ta Bakin 'Yan Mata da Ke Karuwanci

  • Rundunar Amotekun ta ceto wasu ‘yan mata daga gidan karuwa a Ifo, Ogun, inda aka kama mutane 15, ciki har da magajiyar gidan
  • Waɗanda aka ceto sun shaida cewa an yaudare su, sannan aka tilasta su yin karuwanci, inda suke lalata da maza 10 zuwa 12 a rana
  • Wasu 'yan mata biyu, sun yi bayani dalla dalla yadda mai kula da gidan karuwan ta yi masu barazanar kisa idan suka gudu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ogun - Rundunar tsaro ta Amotekun a jihar Ogun ta ceto wasu ‘yan mata daga wani gidan karuwai a karamar hukumar Ifo, a ranar Laraba.

A yayin samamen, an kama mutane 15, ciki har da mai gudanar da gidan karuwan, Idem Joy, a otal ɗin Railway Line da ke tsohuwar hanyar bankin Ifo.

Kara karanta wannan

Sojoji sun firgita 'yan fashi da makami da suka tare hanyoyi a jihar Kaduna

Rundunar Amotekun ta yi magana da ta ceto 'yan mata daga gidan karuwai
'Yan matan da aka ceto daga gidan karuwai a Ogun sun fadi halin da suka shiga. Hoto: @DapoAbiodunCON
Asali: Twitter

'Yan mata masu shekaru 12 zuwa 39 ne ake tilasta su yin karuwanci a wannan sansani, inda ake tsare su ta karfin tsiya, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amotekun ta bankado babban gidan karuwai

Daga cikin abubuwan da aka samu a hannun Idem Joy sun haɗa da kuɗi har N819,600, nau’ukan kwayoyi, fatikin kwaroron roba, da magungunan ƙarfin maza.

Kwamandan Amotekun, Birgediya Janar Alade Adedigba (mai ritaya), ya ce yawan waɗanda aka ceto sun fito ne daga Akwa Ibom.

A cewar Adale, sauran 'yan matan sun fito daga jihohin Cross River da Delta, kuma an tilasta musu yin rantsuwa ta al’ada da kuma tsoratar da su don hana su guduwa.

"Ina lalata da maza 12 a rana" - Matashiya

Wata daga cikin waɗanda aka ceto, ‘yar shekara 14 daga Akwa Ibom, ta ce an yaudare ta da cewa za ta yi aikin sayar da kaya ne a garin.

Kara karanta wannan

Sauƙi ya ƙara bayyana da musulmi suka fara shirye shiryen azumin watan Ramadan

Yarinyar da ko karamar sakandare ba ta kammala ba, ta isa jihar Ogun a ranar 29 ga Janairun 2024, amma aka tilasta mata shiga karuwanci, maimakon sana'ar sayar da kaya.

“Sun ce min aikin sayar da kaya zan yi, don haka na je tare da kawata Glory, amma ita tana aiki a wani otal daban.
"Da muka isa, an ba ni wasu kwayoyi kafin na fara aiki. Ita (Idem Joy) ta yanke wani bangare na gashi na, ta ce idan na gudu za ta kashe ni ta hanyar tsafi da gashin.
“A wasu lokuta nakan samu N20,000 a rana, inda na kan yi lalata da maza 10 zuwa 12 a kowace rana. Suna biyan N1,000 ko N2,000.”

- Inji matashiyar.

An yi wa matashiya barazana da asiri

Wata yarinya ‘yar shekara 17 da aka sakaya sunanta, ta bayyana cewa an kawo ta jihar Ogun a ranar 7 ga Nuwambar, 2024.

Kara karanta wannan

Dan ta'adda ya yi kokuwa da soja domin kwace bindiga a cikin daji

Ta sanar da cewa, an sanya ta yin rantsuwa ta gargajiya, cewa za ta yi aikin karuwanci na tsawon shekara guda kafin ta samu ‘yanci.

“Mafi yawan mazan da nake lalata da su suna biyan N1,000, wasu kuma N2,000 ko N5,000,” in ji ta.

Ta kara da cewa:

“An ce mani idan na gama shekara guda zan samu ‘yanci, sannan za a saya mani waya da akwati cike da kaya.
“Yawanci, nakan yi lalata da maza 10 a rana, amma bayan na gama kuma, sai in ba su dukan kuɗin. Ni a yanzu ina son kawai in koma gida.”

Birgediya Janar Adedigba ya ce za a mika waɗanda aka ceto ga iyayensu, yayin da bincike ke kan gudana don gurfanar da masu laifin a gaban kuliya.

"Na yi lalata da maza 3,000" - Jarumar fim

A wani labnarin, mun ruwaito cewa, jarumar fina-finan Najeriya, Esther Nwachukwu, ta ce ta yi lalata da mazajen aure da ba ta san adadinsu ba.

Kara karanta wannan

CBN ya kawo sabon tsarin cire wa 'yan Najeriya kudi wajen aiki da ATM

A wata hira da aka yi da ita a shirin Nedu Wazobia kwanan nan, jaruma Esther Nwachukwu ta yarda cewa ta yi lalata da maza fiye da 3,000.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.