An bankado wani gidan da 'yan mata masu kananan shekaru ke haihuwa don safarar jariran

An bankado wani gidan da 'yan mata masu kananan shekaru ke haihuwa don safarar jariran

'Yan sandan na sashin binciken manyan laifuka na tarayya (FCIID) sun gano wani gidan karuwai inda aka tara 'yan mata masu kananan shekaru ana yin lalata da su don a sayar da jariran idan sun haihu.

An gano wurin mai suna Dafog Hotel a Shimawa wani gari da ke nan iyakan Legas da Ogun ne a safiyar ranar Laraba inda aka kama maza biyu da mata 14.

Wadanda aka kama sun hada da mai otel din, Gbenga Olayinka, dan uwansa Adekunle Oshineye, wasu karuwai uku - Happiness Daniel, Favour Nkume da Glory Ewelike tare da kuma kananan yara tara.

Kananan 'yan matan sun bayar da sunayensu kamar haka Chisom Onyekwere, Chinonso Okoro, Stella Emmanuel, Gift Wada, Chidinma Emmanuel, Tracy Favour, Success Onu, Comfort Francis, Njoku Divine, Destiny Chibuike da Amanda Chima.

DUBA WANNAN: Kwastam sun gano wani gida da ake canjawa shinkafa buhu, sun kama mutum 15 (Hoto)

The Nation ta ruwaito cewa an kawo kananan 'yan matan ne daga jihohin Akwa Ibom, Kogi, Enugu da Imo inda ake mika su gardawa na zina da su suna biyansu N500 ko N1,000.

Wasu daga cikin 'yan matan suna shaidawa manema labarai cewa suna biyan mai gidansu N1,000 a kullum a matsayin kudin daki kuma sunyi ikirarin cewa kawayensu ne da ke zama a otel din suka janyo su daga kauye.

Bayan ga bayar da su ga gardawa suna zina da su, an gano cewa su ma mazan da ke aiki a otel din suna saduwa da su a duk lokacin da suka ga dama.

Majiyar Legit.ng ta lura cewa mafi yawancin yaran ba su iya rubuta sunayensu ba wadda hakan yasa suka dena zuwa makaranta. An kuma gano cewa ba su san za su iya kamuwa da cututtuka kamar kanjamau da Hepatitis ba da kama kansar mahaifa.

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce an gano wurin ne sakamakon bayannan sirri da rundunar ta samu a daren ranar Talata.

Binciken 'yan sandan ya nuna cewa 16 cikinsu suna zaune a gidan ne suna karuwanci.

Mai otel din, Olayinka ya musanta cewa ana haifan jarirai don safararsu a gidan, ya kuma ce bai san cewa 'yan matan ba su cika shekaru 18 ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel