Dakarun Sojoji Sun Hallaka Kwamandojin 'Yan Ta'adda, Sun Lalata Sansanoninsu

Dakarun Sojoji Sun Hallaka Kwamandojin 'Yan Ta'adda, Sun Lalata Sansanoninsu

  • Dakarun sojojin Najeriya na ci gaba da samun nasarori a yaƙin da suke yi da ƴan ta'adda a yankin Arewa maso Yamma
  • Sojojin na rundunar Operation Fansan Yamma sun samu nasarar hallaka kwamandojin ƴan ta'adda a Sokoto da Zamfara
  • Jami'an tsaron sun kuma lalata sansanonin ƴan ta'addan tare da ceto mutanen da suka yi garkuwa da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yamma sun samu nasarori a yaƙin da suke yi da ƴan ta'adda a yankin Arewa maso Yamma.

Dakarun sojojin sun hallaka wasu manyan kwamandojin ƴan ta’adda tare da rushe sansanoninsu da dama a jihohin Zamfara da Sokoto.

Sojoji sun hallaka kwamandojin 'yan ta'adda
Dakarun sojoji sun kashe kwamandojin 'yan ta'adda a Zamfara da Sokoto Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Mai magana da yawun rundunar Operation Fansan Yamma, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Majalisa ta damu da rashin tsaro a Borno, ta ba gwamnatin tarayya shawara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sojoji suka kai farmakin

Ya ce farmakin an aiwatar da shi ne daga ranar 1 ga watan Fabrairu zuwa 10 ga watan Fabrairu, 2025, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.

Farmakin ya yi matuƙar tasiri wajen kakkaɓe ƴan ta'addan da ke yankunan, wanda hakan ya kawo sauƙin matsalar tsaro ga al’ummomin da abin ya shafa.

Ya bayyana cewa artabun ya fi ƙamari a ƙananan hukumomin Shinkafi da Zurmi na jihar Zamfara, da kuma ƙaramar hukumar Isa ta jihar Sokoto.

An kashe kwamandojin ƴan ta'adda

"Daga cikin shugabannin ƴan ta’adda da aka kashe akwai Kachalla Na Faransa, Dogon Bakkwalo, Auta Gobaje, da Dan Mai Dutsi."
"An kai farmaki kan maɓoyar ƴan ta’adda fiye da 40, ciki har da Tungar Fulani, Unguwar Goga, tsaunin Gangara Hill da Gidan Maji."

- Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi

Baya ga hakan, dakarun sojojin sun samu nasarar ceto wasu mutanen da aka yi garkuwa da su, lamarin da ya kawo farin ciki da sauƙin damuwa ga iyalansu da suka daɗe cikin fargaba.

Kara karanta wannan

Zance ya kare, kotun ƙoli ta yanke hukunci kan bukatar tsige 'yan Majalisa 27

Sojoji za su ci gaba da kakkaɓe ƴan ta'adda

Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi ya sake jaddada cewa rundunar sojojin za ta ci gaba da kai farmaki kan ƴan ta’adda a Arewa maso Yamma da wasu sassan jihar Neja.

Ya buƙaci al’umma da su riƙa ba da bayanai kan maboyar ƴan ta’addan da suka tsere, musamman sanannen ɗan ta’adda, Bello Turji, da muƙarrabansa.

"Wannan nasarar ta Operation Fansan Yamma ta kawo naƙasu ga ayyukan ƴan ta'adda a yankin, kuma ta ƙarfafa ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin Arewa maso Yamma."

- Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi

Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka ƴan ta'adda masu yawa a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yamma.

Sojojin sun hallaka ƴan ta'adda sama da guda 50 tare da raunata wasu da dama a farmakin da suka kai musu a ƙananan hukumomin Shinkafi da Zurmi na jihar Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng