Borno Ta Cika Ta Batse, Zulum Ya Mika Sandar Mulki ga Sabon Sarki, Umar AlKanemi
- Gwamna Babagana Zulum ya miƙa sandar mulki ga sabon Shehun Bama, Dr. Umar Kyari Umar ElKanemi, a wajen taron wani alfarma
- Zulum ya yabawa marigayi Shehun Bama bisa gudunmawarsa ga cigaban Bama tare da fatan sabon Shehun zai ci gaba daga inda ya tsaya
- Sabon Shehun Bama, Umar Kyari ya yi alkawarin goyon bayan manufofin gwamnati don wanzar da zaman lafiya da cigaba mai dorewa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno - Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya miƙa sandar mulki ga sabon Shehun Bama, Dr. Umar Kyari Umar ElKanemi.
Dr. Umar Kyari ya gaji mahaifinsa, Alhaji (Dr.) Shehu Kyari Ibn Ibrahim ElKanemi, wanda ya rasu bayan shekara 30 yana mulkin masarautar Bama.

Asali: Facebook
Zulum ya mika sandar mulki ga Shehun Bama
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Zulum ya taya sabon Shehun murna, yana mai cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Muna da tabbacin cewa da gogewarka za ka jagoranci masarautar cikin nasara da rikon amana kamar mahaifinka."
Gwamnan ya bukaci sabon basaraken ya hada kan al’umma, ya yi aiki tare da duk gidajen sarauta, sannan ya saurari shawarwari masu kyau.
Ya yaba da rawar da sarakunan gargajiya ke takawa wajen karfafa zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’umma daban-daban a jihar Borno.
Gwamna Zulum zai rufe sansanin 'yan gudun hijira
Zulum ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da manufofi don inganta rayuwar jama’a, bisa tsarin bunkasar jihar na shekaru 25.
Gwamnan ya sanar da shirin rufe sansanin 'yan gudun hijirar Bama da sake tsugunar da mutanen yankunan Daral Jamal, Tarmua, Mayanti, Bula Yobe da Kumshe.
Zulum ya ce an riga an saki kudi don dawo da wutar lantarki a Bama, tare da alkawarin cewa Gwoza za ta samu wutar lantarki nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan
'Ka taka masa birki': An kai karar El Rufai gaban Nuhu Ribadu, an hango hatsarin kalamansa
Borno: Zulum ya yabawa Kashim Shettima
Ya yaba wa marigayi Alhaji Kyari Ibn Umar, wanda ya taka rawar gani a bangarorin ilimi, kiwon lafiya, zaman lafiya, da wayar da kan jama’a.
Gwamnan ya bayyana tabbacin cewa sabon Shehun Bama zai gina kan nasarorin da mahaifinsa ya bari.
Ya gode wa mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, bisa jagorancin da ya bayar wajen farfado da garin Bama.
Zulum ya yi godiya ga sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III, Shehun Barno, da sarakunan gargajiya daga Najeriya, Kamaru da Chadi da suka halarci taron.
Sabon Shehun Bama ya dauki alkawura
A jawabinsa, Dr. Umar Kyari, ya yi alkawarin gina fahimta a tsakanin jama'a, marawa manufofin gwamnati baya, da karfafa zaman lafiya mai dorewa.
Ya gode wa Gwamna Zulum bisa sake mayar da mutanen da rikici ya shafa zuwa ga muhallansu, tare da ba su kayan noma da tallafi.
Kalli hotunan bikin mika sandar a kasa:

Kara karanta wannan
'Shi zai iya gyara Najeriya': Dan PDP ya roki Kwankwaso, Obi su hade da Atiku Abubakar
An nada sabon shehun Bama
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Alhaji Umar Ibn Kyari Al Amin El-Kanemi ya zama sabon Shehun Bama, bayan rasuwar mahaifinsa, Alhaji Kyari Ibn Umar El-Kanemi.
Sakataren gwamnatin Borno, Alhaji Usman Jidda Shuwa, ya mika wasikar tabbatarwa ga sabon sarkin masarautar a ranar Litinin, 4 ga Mayu, 2020.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng