Borno: Sabon Shehun Bama ya kai wa Gwamna Zulum ziyarar ban girma (Hoto)

Borno: Sabon Shehun Bama ya kai wa Gwamna Zulum ziyarar ban girma (Hoto)

Sabon Shehun Bama, Shehu Umar II El-Kanemi, ya kai wa gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ziyara ta ban girma domin yin mubaya a bayan nada shi sarauta.

Gwamna Zulum ya nada Shehu Umar II ne a matsayin sabon Shehun Bama a ranar 4 ga watan Mayun 2020 bayan rasuwar mahaifinsa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A yayin da ya ke tarbar sarkin a gidan gwamnati a Maiduguri a ranar Laraba, Gwamna Zulum ya mika godiyarsa ga Shehun saboda ziyarar ya kuma zaburar da shi bisa babban aikin da ke gabansa.

Zulum, ya kuma gargadi cewa ba za a amince wani sarki ya rika mulkar jiharsa daga kasar waje ba.

Borno: Sabon Shehun Bama ya kai wa Gwamna Zulum ziyarar ban girma
Borno: Sabon Shehun Bama ya kai wa Gwamna Zulum ziyarar ban girma. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Katsina: An yanke wa dattijo dan shekara 70 da ya zazzagi Buhari hukunci

Gwamna Zulum ya ce, "Ba zan amince wani sarki ya rika mulki daga wata kasar ba, gwamnatin Borno ba za ta amince wani sarki ya rika mulki daga wani garin ba.

"Na zauna a Bama na tsawon watanni shida a lokacin da na ke Kwamishina, babu abinda ya faru da ni."

Gwamna Zulum ya shaidawa sabon sarkin cewa masu nadin sarakuna na masarautar Bama ne suka bayar da shawarar a nada shi.

Zulum ya ce, "Bayan zaben ka da masu nadin sarki suka yi, na tuntubi mutane da dama a masarautar Bama da wajen masarautar.

"Ina farin cikin sanar da kai cewa kashi 95 cikin 1OO da na tuntuba sun goyi bayan nada ka."

A jawabinsa, sabon sarki Shehu Umar II El-Kanemi ya mika godiyarsa ga Gwamna Zulum saboda nada shi sarkin Bama.

Ya tabbatar masa cewa ba zai bashi kunya ba.

Sarkin ya ce, "Mai girma gwamna, Na kawo wannan ziyarar ne domin mika godiya ta gareka tare da sanar da kai cewa mun zabi ranar nadin sarauta ranar Asabar May 9, 2020 in Bama Insha-Allah."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel