Muhimman abubuwa 7 da ba kowa ya sani ba game da sabon Sarkin Bama

Muhimman abubuwa 7 da ba kowa ya sani ba game da sabon Sarkin Bama

A ranar Asabar 9 ga watan Mayun 22 ne aka yi bikin nadin sabon Shehun masarautar Bama, Umar Shehu Kyari.

Sabon sarkin shine da na farko ga tsohon sarkin Bama, marigayi Kyari Umar Ibrahim El-kanemi.

An saka masa sunan kakansa ne, marigayi Shehun Dikwa, Umar Ibn Ibrahim El-kanemi.

An nada shi a matsayin Shehun Bama na biyu ne a ranar Litinin 4 ga watan Mayun 2020 don ya gaji sarautar mahaifinsa.

Muhimman abubuwa 7 da ba kowa ya sani ba game da sabon Sarkin Bama
Muhimman abubuwa 7 da ba kowa ya sani ba game da sabon Sarkin Bama
Asali: Twitter

Ga wasu muhimman abubuwa a kan sabon sarkin da ba kowa ya sani ba.

1. An haife shi a ranar 8 ga watan Janairun 1983 kuma ya girma a karamar hukumar Bama ta jihar Borno.

2. Ya yi karatiun frimari a Bama. Ya kuma yi fara sakandare a Kwallejin Gwamnati na Maiduguri kana daga bisani ya koma Foundation Secondary School a Maiduguri.

3. Ya yi karatun Diploma a fanin koyan aikin lauya a Kwallejin Ilimi ta Kimiyya da Fasaha ta Umar Ibn Ibrahim da ke Bama.

DUBA WANNAN: Dokar kulle: Limamai za su share gidan hakimi na sati daya a Kano

4. Kafin nadinsa a matsayin sarki, shine shugaban kamfanin Bimmbazz (BSBG) Nigerian Limited kuma dan kasuwa ne.

5. Yana da aure da yaya hudu

6. Yana sha'awar hawa doki, tafiye tafiye da wasan badminton.

7. Ya ziyarci kasashen duniya da dama da suka hada da Chad, Kamaru, Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, (U.A.E), Misra, Indiya, Birtaniya da sauransu.

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno zai kafa ofishi a kauyen Auno da ke karamar hukumar Konduga na jiharsa domin karfafa wa mutanen kauyen gwiwa da suka gudu saboda tsoron yan ta'adda su dawo gida.

A yayin da ya kai ziyara kauyen a ranar Asabar, Zulum ya ce zai rika amfani da ofishin daga lokaci zuwa lokaci domin karfafawa mutanen kauyen gwiwa su dawo gida.

Ya ce hakan na da muhimmanci sosai duba da kusancin da Auno ke da shi da babban birnin jihar da kuma Jami'ar jihar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnan ya bukaci a kara samar da jamian tsaro a kauyen domin hakan zai karfafa wa mutane gwiwa.

Ya kuma umurci Ma'aikatar Sake Gina Garuruwa ta Tallafawa wadanda Iftilai ya fada musu ta yi gaggawar samar da abinci da kudi ga wadanda suke zaune a garin a halin yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel