'Yan Najeriya na Fuskantar Barazana daga Trump, Amurka Ta Dakatar da Ayyukan USAID

'Yan Najeriya na Fuskantar Barazana daga Trump, Amurka Ta Dakatar da Ayyukan USAID

  • Dakatar da ayyukan USAID da gwamnatin kasar Amurka ta yi, ya kawo cikas wajen rarraba kayan ba da tazarar iyali a Bauchi
  • Dakta Rilwanu Mohammed ya ce USAID ke rarraba kayan zuwa Bauchi, amma an dakatar da hakan saboda umarnin Donald Trump
  • Sakamakon hakan, gwamnatin jihar Bauchi ta ware Naira miliyan 50 don tallafa wa UNFPA wajen samar da kayan tsara iyali ga cibiyoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi - Dakatar da ayyukan USAID bisa umarnin Shugaban Amurka, Donald Trump, ya shafi shirin ba da tazarar haihuwa a jihar Bauchi.

Shugaban hukumar kula da lafiya daga matakin farko a Bauchi, Dakta Rilwanu Mohammed, ya ce dakatarwar ta kawo cikas ga rarraba kayan tsara iyali.

Umarnin Trump na dakatar da USAID ya jawo matsala ga shirin tazarar haihuwa a Bauchi.
Shirin tazarar iyali a jihar Bauchi na fuskantar barazana saboda umarnin Trump. Hoto: Getty Images/ Petri Oeschger, Anna Moneymake and Anadolu.
Asali: UGC

Dakta Rilwanu ya ce wannan dakatarwa ta haifar da matsaloli wajen samun wadatattun kayan tsarin iyali a cibiyoyin kiwon lafiya, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Kano, gobara ta kashe dabbobi 78, ta lalata kayan abinci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dakatar da aikin USAID ya jawo cikas a Bauchi

Likitan ya yi wannan bayanin ne yayin ziyarar neman goyon baya da ƙungiyar J4PD ta kai masa a ranar Alhamis a jihar Bauchi.

Shugaban hukumar cibiyon kiwon lafiyar ya ce USAID ce ke da alhakin raba kayan tsarin iyali har zuwa cibiyoyin kiwon lafiya a Bauchi.

“Tun bayan dakatarwar, cibiyoyin kiwon lafiya suna fama da ƙarancin kayan, yayin da aka samu ƙarin buƙatar kayan ba da tazarar haihuwar."

- Dakta Rilwanu Mohammed

Umarnin Trump na barazana ga tazarar haihuwa

Dakta Rilwanu ya kara da cewa hukumar ta fara tarurruka don tabbatar da cewa kayan sun isa duk cibiyoyin lafiya ba tare da an karkatar da su ba.

Ya nuna damuwa kan umarnin Donald Trump na dakatar da ayyukan USAID, yana mai cewa lamarin ya yi mummunan tasiri kan ayyukan tsarin iyali a jihar.

Mohammed ya bayyana cewa gwamnatin Bauchi ta ware Naira miliyan 50 a matsayin tallafin haɗin gwiwa da UNFPA don samar da kayan tsarin iyali a yanzu.

Kara karanta wannan

Rusau: Abba zai kashe biliyoyi wajen yin asibiti, tituna, lantarki a Rimin Zakara

USAID: Amurka ta ba Najeriya tallafin $7.8bn

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Amurka ta ba Najeriya tallafin dala biliyan 7.8 a cikin shekaru goma da suka gabata.

Tallafin Amurka ya taka rawar gani wajen taimakawa Najeriya, musamman wajen inganta rayuwa da bunkasa ci gaban al’umma.

Yawancin tallafin ya fi mayar da hankali kan fannonin lafiya, tsaro da ci gaban tattalin arziki don shawo kan matsalolin gaggawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel