Babu wani maganar tsarin iyali a Addinin Musulunci Inji Honarabul Gudaji Kazaure

Babu wani maganar tsarin iyali a Addinin Musulunci Inji Honarabul Gudaji Kazaure

- Dan Majalisar Jihar Jigawa Gudaji Kazaure yayi magana game da tsarin iyali

- Honarabul Gudaji Kazaure yace bai dace a tilastawa Musulmai wannan harka ba

- A cewar sa addini Musulunci bai yarda da tsarin iyali ba don haka bai dace ba

Za ku ji cewa Dan Majalisar Jihar Jigawa Hon. Gudaji Kazaure yayi magana game da tsarin iyali a Najeriya. Kazaure yace tsarin iyali fito na fito ne da Annabin Allah.

Honarabul Muhammad Gudaji Kazaure yace bai dace a tilastawa Musulmai wannan harka na tsarin iyali ba a lokacin da aka kawo maganar a Majalisa. Dan Majalisar na Yankin Kazaure da kewaye yayi watsi da lamarin na tsara iyali yace bai dace ba.

KU KARANTA: Ana bukatar Nnamdi Kanu a Kotu a yau dinnan

Gudaji Kazaure ya tofa albarkacin bakin sa ne inda har ya jawo wani Hadisi daga bakin Annabi Muhammad SAW wanda yayi umarni a hayayyafa domin al'ummar sa tayi yawa har yayi alfahari da ita a Ranar gobe kiyama.

Dan Majalisar dai yace idan aka ce kowa ya tsare iyalin sa hakan na nufin an yi na fito da Sunnar Manzon Allah mai aminci da yarda. Gidan labarin na OAK ne ya dauki bidiyon da Dan Majalisar yayi wannan jawabi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng