Za a sanya dokar tazarar haihuwa a jihar Kano

Za a sanya dokar tazarar haihuwa a jihar Kano

- Wahala da talauci da kuncin rayuwa da al'ummar jihar Kano su ke ciki ta tilasta Sarkin Kano Muhammad Sanusi II, fito da kudurin tsarin tazarar haihuwa a fadin jihar

- Sarkin ya ce ya gama shiri tsaf, abinda ya rage kawai shine ya gabatar da dokar ga gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje

Sarkin Kano Muhammad Sanusi II, ya bayyana cewa sun gama shirye-shirye tsaf na gabatar da dokar tsarin tazarar haihuwa ga gwamna Abdullahi Umar Ganduje, domin mai da tsarin doka a jihar Kano.

Sarkin ya bayyana hakan jiya, a wurin wani taron tattaunawa da suka gabatar a Kano, ya ce za a gabatar da tsarin ne don magance kalubalen da ake fama dashi a kasar Hausa na tsarin iyali, da kumaa matsalar tsaron da ake fama da ita a yankuna da dama na kasar nan.

Sarkin ya ce ya fahimci cewa al'umma ba za su fahimci inda ya sa gaba ba akan wannan ra'ayi nashi, shi ne yasa ya yanke shawarar kafa kwamiti ta lauyoyi da malamai domin gabatar da kudurin nashi.

Za a sanya dokar tazarar haihuwa a jihar Kano
Za a sanya dokar tazarar haihuwa a jihar Kano
Asali: Facebook

Ya ce ko da yake a yanzu ya samu kashi 80 cikin 100 na dokar da ya ke so ya kafa din, amma idan har aka shigar da tsarin cikin dokar kasa, zai magance matsalolin tattalin arziki a jihar Kano.

Sarki Sanusi ya yi fatan gwamna Ganduje ya samu ya shawo kan 'yan majalisarsa don tabbatar da shigar da tsarin ya zama doka a jihar, ya kara da cewa shugaban kasar Jamhuriyar Niger ya ziyarce shi, inda ya bayyana cewa shima yana jira ne a gabatar da dokar domin ya fara amfani da ita a kasar shi.

Sarkin ya bayyana cewa idan ba dauki mataki akan matsalar talaucin da ke addabar kasar nan ba, Najeriya da Jamhuriyar Demokiradiyar Congo za su dauki kashi 40 cikin dari na mutanen da ke fama da talauci a fadin duniya nan da shekarar 2050.

KU KARANTA: Dangote ya bayyanawa matasa hanyar da za su zama kamar shi

Sarkin ya bayyana cewa a shekarar 2050, nahiyar Afirka za ta kasance da kashi 86 cikin dari na mutanen da ke fama da matsanancin talauci a duniya, kuma Najeriya za ta dauki rabi a cikin kashi 86, inda za ta zamanto kasar da tafi kowacce kasa talauci a duniya.

Ya danganta matsayin da ake ciki yanzu na yawan haihuwa da ake, inda zaka taradda mace ta haifi 'ya'ya takwas ita daya, idan kuma mijin mata hudu ne dashi a karshe sai ka ganshi da yara 32, wadanda za su taso cikin talauci da yunwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel