Rahoto: Manyan Matsaloli 3 da Suka Hana Yara Miliyan 15 Zuwa Makaranta a Arewa
- Ilimi a Arewacin Najeriya na fuskantar manyan kalubale, musamman rashin tsaro, talauci, da al’adun da ke hana yara zuwa makaranta
- Duk da cewa gwamnati, kungiyoyin kasa da kasa da ma na Najeriya na kokari don magance matsalar, akwai aiki mai yawa a gaba
- Wannan makalar ta yi bayani dalla dalla kan matsalolin da ilimi ke fuskanta a Arewa, da kuma hanyoyin magance su cikin sauki
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ilimi wanda shi ne gishirin zaman duniya na fuskantar manyan kalubale a Arewacin Najeriya, inda miliyoyin yara ba sa samun damar zuwa makaranta.
Wannan matsalar ta kara tsananta sakamakon rashin tsaro, al’adu, da talauci, inda ake ganin za ta iya hana ƙarnin yara na gaba samun damar yin ilimi.
Girman matsalar ilimi a Arewa
Arewa ta fi sauran yankunan Najeriya yawan yaran da ba sa zuwa makaranta. Rahoton UNICEF ya nuna cewa, yara sama da miliyan 10 a yankin ba sa zuwa makaranta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matsalar ta fi kamari a jihohi kamar Borno, Yobe, da Adamawa sakamakon hare-haren Boko Haram, wanda ya tilasta hijirar dalibai da lalata ginin makarantu.
Rashin tsaro ya jawo gwamnoni da dama sun rufe makarantu domin kare rayuka da lafiyar dalibai, duk da cewa wasu makarantun an fara bude su zuwa yanzu.
A wani bangaren kuma, wannan matsalar ta ƙara muni sakamakon rashin kayan koyo da koyarwa a kauyuka, yayin da wasu kauyukan kuma ba su ma da makarantun.
Abubuwan da suka tsananta matsalar ilimi
Matsalar tsaro a Arewacin Najeriya
Harkokin tsaro a Arewacin Najeriya na daya daga cikin manyan kalubale wajen samun ilimi.
Rahoton Human Rights Watch ya alakanta hakan ga hare-haren da ƙungiyoyin 'yan ta'adda ke kaiwa a makarantu, sace malamai da dalibai da sauransu.
Wannan tilasta an rufe makarantu da dama a yankunan da ke karkashin ikon Boko Haram ko ke fuskantar yawaitar hare hare domin kare dalibai da malaman.
Talauci a matsayin babban kalubale
Talauci na daga cikin babban kalubale wajen samun ilimi a Arewa.
Rahoton Bankin Duniya na 2022 ya nuna cewa fiye da kashi 70% na al’ummar Arewacin Najeriya na rayuwa a cikin talauci.
Matsin tattalin arziki ya sanya iyalai da dama sun fi ba neman abinci da yadda za su kula da rayuwarsu fifiko fiye da tura yaransu zuwa makaranta.
Rashin abinci da rayuwa mai kyau yana tilasta wa yara neman hanyoyin neman kudi ta wasu hanyoyi, kamar sayar da kaya a tituna ko yin kwadago, maimakon zuwa makaranta.
Tasirin al’adu a ilimin Arewa
Al’adu na taka muhimmiyar rawa wajen ƙara tsananta matsalar ilimi, musamman rashin ganin darajar ilimin 'ya'ya mata.
A wasu sassan Arewa Najeriya, ana kallon auren wuri a matsayin wani muhimmin abu ga mata, wanda ke hana su damar ci gaba da karatu.
Yawancin lokaci, shawarar auren wuri tana tasiri daga ƙoƙarin kare 'yan mata daga lalacewa ko tsufa ba tare da aure ba, to sai dai kuma hakan yana hana matan samun ilimi da ci gaba.
Rahoton UNICEF ya nuna cewa hudu daga cikin mata goma a Najeriya ana aurar da su ne kafin su kai shekara sha takwas, wanda wannan matsalar ta fi kamari a Arewa.
Kokarin gwamnati da kungiyoyi kan ilimi
- Matakan da gwamnati ta dauka
A matsayin martani ga tabarbarewa ilimi, gwamnatin Najeriya ta aiwatar da shirye-shirye daban-daban da nufin inganta ilimi a Arewa da Najeriya baki daya.
Daya daga cikin wadannan matakai shi ne shirin Safe Schools, wanda aka kaddamar a shekarar 2014 bayan garkuwar da aka yi da daliban Chibok.
Wannan shiri ya mai da hankali kan gina makarantu a wuraren da rikici ya shafa da kuma samar da yanayin koyo mai tsaro ga yara.
A cewar rahoton Nduka Okolo Obasi da aka wallafa a Research Gate, shirin ciyar da yara abinci ya taimaka wajen karfafa zuwan yara makaranta, musamman a yankunan karkara.
An fara aiwatar da shirin NHGSFP a shekarar 2004 kuma an sake kaddamar da shi a 2016 inda ake ba 'yan makaranta abincin rana a kullum.
- Tallafin da kungiyoyin duniya suka bayar
Kungiyoyin duniya kamar UNICEF, gidauniyar Malala da sauransu suma suna taka muhimmiyar rawa wajen magance matsalar ilimi.
Misali, gidauniyar Malala ta yi aiki a Arewacin Najeriya wajen inganta ilimin mata da kokarin canza manufofi da ke goyon bayan tabbatar da ilimin 'yaya mata da ci gaba da karatunsu.
A cewar rahoton gidauniyar Malala na baya-bayan nan, 'yan mata ne ke da kashi 38 cikin 100 na yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya inda abin ya fi kamari a Arewa.
- Korin kungiyoyin cikin gida kan ilimi
Kungiyoyin tallafi na cikin gida (NGOs) suma sun taka irin tasu muhimmiyar rawar wajen cike gibin da gwamnati ta bari a magance matsalar ilimi.
Misali, kungiyar Save the Children tana kafa cibiyoyin koyo na wucin gadi a sansanonin 'yan gudun hijira a Arewa maso Gabas don ba wa yara damar cigaba da karatu.
Har ila yau, kungiyar na cikin shirin tallafin Tarayyar Turai na kai dauki a jihar Borno da ke da nufin kara karfafa tsarin ilimi da aiyuka a yankunan da rikici ya shafa a jihar.
Aiki na gaba: Abin da ya kamata a yi
Duk da irin kokarin da gwamnati da kungiyoyi ke yi, akwai bukatar ƙara zuba jari da ƙoƙari wajen warware matsalar ilimi a Arewacin Najeriya.
Dole ne gwamnati ta kara ƙoƙari wajen samar da tsaro a makarantu da arziki, sannan a magance tushen matsalar, kamar auren wuri, wanda ke hana mata samun ilimi.
Al’umma za su iya taka rawa mai muhimmanci wajen inganta ilimi ta hanyar tallafawa matakan gwamnati na ilimi da kuma sama wa kansu mafita daga gida.
Hakanan, kungiyoyi na ƙasa da ƙasa na da muhimmiyar rawa wajen tallafawa shirye-shiryen ilimi a Arewacin Najeriya.
Gyaran ilimi a mahangar masanan Arewa
Mallam Isa Abubakar, wani mai sharhi kan harkokin ilimi a Arewa maso Gabas, ya shaidawa Legit Hausa cewa rikon sakainar kashin da ake yiwa malamai ya jawo tabarbarewar ilimi.
Malamin ya ce ana samun yara da dama da ke fita daga makaranta saboda matsin tattalin arziki, inda suka fi ba da fifiko ga neman abinci ko kudin tafiyar da rayuwarsu.
Mallam Isa ya yi nuni da cewa rashin ayyukan yi ga dumbin wadanda suka kammala karatu ya sa darajar ilimi ta ragu a idon masu tasowa, wadanda ke ganin yin ilimi ba shi da amfani.
"Ko da gwamnati ta sanya ilimi ya zama kyauta, a yadda ake ciki, misali a Arewa maso Gabas, yara ba za su yi ilimi mai kyau ba saboda rashin abinci, ruwa mai tsafta, wutar lantarki da sauransu.
"Ko da yaro ya zo makarantar, hankalinsa na can wani waje. Ana kama yara suna satar kayan makaranta suna sayarwa saboda su nemi abin da za su ci."
- A cewar Mallam Isa.
Malamin ya ce iyaye da dama yanzu ba sa iya biyan kudin makarantar yaransu, ko sayen litattafai da sauran kayan karatu, wanda hakan ke barazana ga ilimi mai inganci.
Mai sharhi kan harkokin ilimin ya ce wata matsala babba ita ce yadda ake yiwa malamai rikon sakainar kashi, ta fuskar rashin wadataccen albashi ko alawus.
Mallam Isa Abubakar ya ce:
"Malami yana karantarwa a makarantar gwamnati amma ana ba shi N30,000 ko makamancin haka, ta ya zai rayu da iyalansa? Ka ga dole sai an gyara masu ilimi kafin ilimi ya yi daraja.
"Idan har aka bar malamai a wulakance, babu albashin kirki, babu dan babur din hawa ka sutura mai kyau, to babu yadda za ayi dalibi ya ji sha'awar yin ilimi har ya zama kamar malamin."
Mallam Isa ya ce wajibi ne gwamnati ta bunkasa rayuwar malamai domin dawo da martabar ilimi sannan a magance matsalar tattalin arziki da ke addabar al'ummar kasar.
Rufewa: Hanya mai dorewa a mahanga ta
Matsalar ilimi a Arewa Najeriya na buƙatar haɗin gwiwa daga kowane sashe na al'umma.
Duk da cewa an samu ci gaba, har yanzu akwai aiki a gaba kafin a tabbatar da cewa kowanne yaro a Arewa zai samu ilimi mai zurfi.
Amma da ci gaba da jajircewar gwamnati, kungiyoyi, al'umma, da kungiyoyin ƙasa da ƙasa, wata alama ce ta kyakkyawar makomar ilimi ga yaran Arewa.
Ilimi na daga cikin muhimman abubuwan da za su kawo ƙarshen talauci, matsalar tsaro da bambance bambance, kuma shine makullin ƙirƙirar makoma mai kyau ga Arewa Najeriya.
Illar rashin ilimin yara a shiyyar Arewa
A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya (AGF) ta koka kan cewa rashin ilimin yara a jihar ya haifar da karuwar matsalar rashin tsaro.
Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Gombe, Yahaya Inuwa ya ce adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a Arewa ya fi yawa fiye da na shiyyar Kudu.
Asali: Legit.ng