Ilimin Boko a Arewa, ci gaban mai hakar rijiya, sharhin jaridar The Guardian

Ilimin Boko a Arewa, ci gaban mai hakar rijiya, sharhin jaridar The Guardian

Legit.ng ta kawo muku sharhi daga Jaridar 'The Guardian' akan ilimin Boko a arewacin Najeriya duk da tallafin ilimi da ake badawa.

'Sama da rabin yaran duniya da basa zuwa makaranta 'yan Najeriya ne.' Gwamnatin Najeriya

Da yawan Jahohi a arewacin Najeriya an bar su a baya a shekaru da yawa a cikin Jahohi 36 na Kasa a fannin cigaban ilimi. Kuma a duk cikin wannan matsalar babu ta rashin tallafin kudi. A kwanan nan Ofishin (NBS) ya fitar da kasafin yadda tazarar ci gaban ilimi take a tsakanin jahohin Kudu da na Arewa.

Mafi akasarin mutanen da basu iya rubutu da karatu ba daga Jahohin Arewa suke. Jihar Yobe tafi karancin masu ilimi a lissafin NBS, tana da kason 7.23%. Jahar Zamfara ta biyo bayan Yobe da 19.16%, sai Katsina 10.36%, Sokoto 15.01%, Bauchi 19.26%, Kebbi 20.51% da Niger 22.88%. Jahar Taraba ce kawai ta fita zakka da take da 72 %.

Idan kuma aka kwatanta da Jahohin Kudu; Imo tafi sauran yawan masu Ilimi tana da 96.43%, sai Legas ta biyo ta da 96.30%, sai Ekiti 95.79%, Ribas 95.76%, Abia 94.24%, Anambra 92.11%, Osun 90.57%, Edo 90.53%, Enugu 89.46% da Cross River me 89%.

Ilimin Boko a Arewa, ci gaban mai hakar rijiya, sharhin jaridar The Guardian
Ilimin Boko a Arewa, ci gaban mai hakar rijiya, sharhin jaridar The Guardian

Duk da rashin ci gaban ilimin arewa bai kai na kudu ba, Gwamnati bata daina fitar da kudaden da take fitarwa duk wata na ka’ida ba na tallafin ilimi.

A cikin shekaru goma da suka wuce, Gwamnonin Jahohi a arewa sun karbi kudi a lissafe har tiriliyan goma sha biyu. Sama da rabin Jahohin arewa ne suka anfana da kudin. Jahar Yobe da take da karancin masu ilimi ta karbi naira biliyan 30, Imo da ta nunka ta a yawan Jama’a yawan masu ilimi ta karbi biliyan 29.

DUBA WANNAN: Jaridar The Economist ta yi sharhi kan rashin lafiyar Buhari a Ingila

A wani bincike a shekarar 2011 ya nuna Jahohin arewacin Najeriya sun fi sauran Jahohin yawan yara da basa zuwa makaranta. Duk da tallafin ilimin da ake badawa, akwai sama da almajirai miliyan tara a arewa. Yawan ‘ya’ya mata a arewa masu zuwa makaranta bai fi 25% ba in aka danganta da na kudu da suke da 75%.

Yakin boko Haram a Arewa maso gabas yana daya daga cikin manyan matsalolin da suka janyo karin raguwar ilimi a arewa. A arewa dai akwai masu yaki da ilimi, banda masu makamai na ta'adda, akwai iyaye da suke yaki da kai ‘ya’yansu makaranta.

Kari da makarantun Gwamnati a shekarun nan suna janyo rashin samun wadataccen ilimi. Gwamnati bata mai da hankali akan ganin cigaban makarantunta. hakan ya janyo yara basu da makarantun da zasu je sai yawon talla da almajiranci.

Kungiyar UNICEF tace 'sama da kashi 60 na yaran da basa zuwa makaranta 'yan arewa ne.' Kungiyoyin UN da UNICEF suna kokarin ganin an shawo kan matsalar ilimi a arewa da sauran matsalolin Najeriya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng