Abubuwa 4 da ke zama cikas ga ilimin 'ya mace a arewacin Najeriya

Abubuwa 4 da ke zama cikas ga ilimin 'ya mace a arewacin Najeriya

Ilimin ‘ya mace abune mai muhimmanci ga kowani kasa da yanki a duniya. Wannan ya zama batun muhawara tsakanin jama’a saboda kalubalen da ilimin ‘ya mace ke fuskanta musamman a arewacin Najeriya.

Abubuwa 4 da ke zama cikas ga ilimin 'ya mace a arewacin Najeriya
Abubuwa 4 da ke zama cikas ga ilimin 'ya mace a arewacin Najeriya

Ga abubuwan 4 wanda suka zama cika ga ilimin ‘ya mace a arewacin Najeriya:

1. Talauci

Game da binciken, kasha 28 cikin 100 sunyi imanin cewa talauci ne babban cikas ga ilimin diya mace a Najeriya.

A arewacin Najeriya kuwa, ko shakka babu shine babban umuul khaba’isi. Talauci ne ke sanya iyaye na aika yaransu mata talla wanda ke hanasu zuwa makaranta.

2. Al’ada

A arewacin Najeriya, al’adanmu tayi babban tasiri akanmu. Wanda ya shafi a cigabanmu da kuma wayewanmu.

Duk da cewa anyi ittifakin cewa ilimantar da diya mace nada muhimmanci ga al’umma, har ila yau akwai iyaye wadanda suke hana yara matansu karatu.

KU KARANTA: Majalisa ko DSS basu isa su hana ni yaki da rashawa ba- Magu

Game da cewan wasu, ai aikin mace shine kula da gida. Duk da cewa addinin musulunci ya wajabta neman ilimi da ilimantar da iyali da yara, wannan kalubale bai gushe a arewa ba.

3. Rashin sani a bangaren iyaye

Bincike ta nuna cewa kasha 18 cikin100 sun amince da cewa jahilcin iyaye babban kalubale ne. kasha 25 sunyi imanin cewa idan aka ilimantar da iyayen, zasu fahimici muhimmancin ilimantar da ‘ya mace.

Wani sakamakon rashin ilimin a bangaren iyaye shine, a tunaninsu idan ‘ya mace tayi karatu, ba zata amfanesu da shi, illa mijinta da yaranta. Saboda haka, sai su mayar da hankali wajen ilimantar da yara maza.

4. Saurin aure

Kasha 15 na mutane sun imanin cewa babban kalubalen da ke zama cikas ga ilimin ‘ya mace shine aurar da su da akeyi da wuri.

A wasu wurare a arewa, ana aurar da yara mata kafin su san ciwon kansu. Kana kuma ana aurar da su ga jahilan mazaje wadanda ba zasu ilimantar da su bayan aurensu ba. wannan sai ya haifar da zuriya jahila.

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel