Jerin sunayen 'yan matan Chibok 112 da har yanzu ke hannun Boko Haram
- A shekarar 2014 'yan ta'addan Boko Haram suka sace daliban makarantar 'yan mata ta Chibok a jihar Borno
- Wasu daga cikin daliban sun kubuta, wasu an sako su wasu kuwa an gano cikin rubibi a tsawon shekarun
- A cika shekaru 7, kungiyar fafutuka ta Bring Back Our Girls ta bayyana sunayen wadanda suke hannun Boko Haram
A ranar 14 ga Afrilu, 2014, Mayakan Boko Haram suka mamaye Makarantar Sakandaren ’Yan mata ta Gwamnati dake Chibok a jihar Borno, inda suka sace 'yan mata 276 da ke shirin rubuta jarabawar su ta karshe na sakandare, TheCable ta ruwaito.
Daga cikin su, 164 daga ciki ko dai sun tsere, an sako su ko an samo su - amma tsawon shekaru bakwai da wannan aika-aikatar, 'yan mata 112 har yanzu suna hannun 'yan ta'addan.
Kungiyar ‘Bring Back Our Girls’ (BBOG) ita ce kan gaba a yakin neman dawo da daliban da aka sacen tun lokacin da aka sace su.
KU KARANTA: Jihar Adamawa ta dakatar da albashin malamai sama da 2,000 da zargin na bogi ne
A ranar Asabar, kungiyar ta BBOG reshen jihar Legas ta gudanar da zaman dirshan a yankin Ikoyi da ke jihar don nuna jimamin cika shekara bakwai da sace yaran.
A yayin zaman, kungiyar ta bayyana sunayen ‘yan matan Chibok 112 da har yanzu ke hannun Boko Haram.
'Yan matan 112 sun hada da:
1. Aisha Lawan
2. Hauwa Mutah
3. Falta Lawan
4. Hajara Isa
5. Kabu Mala
6. Maryam Abba
7. Hannatu Musa
8. Laraba John
9. Deborah Nuhu
10. Saratu Dauda
11. Aisha Grema
12. Asabe Ali
13. Margret Shettima
14. Yana Yidau
15. Hauwa Kwakwi
16. Hauwa Musa
17. Saraya Musa
18. Hauwa Joseph
19. Yana Pogu
20. Jinkal Yama
21. Eli Ibrahim
22. Rifkatu Yakubu
23. Hannatu Nuhu
24. Maryamu Abubakar
25. Hamsatu Abubakar
26. Deborah Abbas
27. Rhoda Haruna
28. Hauwa Wuleh
29. Hauwa Nkeki
30. Christiana Yusuf
31. Raklya Kwamta
32. Christiana Yusuf
33. Halima Gambo
KU KARANTA: Abubawan da ke jawo hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya
34. Rhoda John
35. Hassana Adamu
36. Ruth Ngiladar
37. Safiya Abdu
38. Serah Luka
39. Aishatu Musa
40. Hauwa Peter
41. Ruth Bitrus
42. Hanatu Ishaku
43. Mary Amos
44. Victoria Dauda
45. Saratu Thuji
46. Mary Dauda
47. Saratu Iliya
48. Halima Ali
49. Bilkisu Abdullahi
50. Rebecca Ibrahim
51. Zainab Yaa
52. Awa Ali
53. Hanatu Madu
54. Sarah Samuel
55. Mary Nkeki
56. Hauwa Isuwa
57. Godiya Bitrus
58. Awa Sasa
59. Hauwa Balte
60. Glory Yaga
61. Mary Paul
62. Ladi Paul
63. Ruth Lawan
64. Laraba Mallum
65. Ruth Wavi
66. Rahila Yohanna
67. Ihyi Abudu
68. Lydia Simon
69. Zara Ishaku
70. Rejoice Sanki
71. Deborah Abari
72. Sikta Abudu
73. Saraya Ali
74. Maryamu Lawan
75. Esther John
76. Ladi Joel
77. Lydia Emmar
78. Rose Daniel
79. Hauwa Abdu
80. Laraba Paul
81. Esther Ayuba
82. Mary Dauda
83. Margret Watsal
84. Miriam Jafaru
85. Kuma Solomon
86. Agnes Dauda
87. Mary Dama
88. Patience Jacob
89. Tabi Thomas
90. Hauwa Tella
91. Maryamu Yahaya
92. Saraya Stover
93. Jummal Aboku
94. Elizabeth Job
95. Suzana Yakubu
96. Mary Sule
97. Saratu Thauji
98. Ladi Wadal
99. Yayi Abana
100. Kwamta Kabu
101. Grace Amadu
102. Saraya Paul
103. Esther Markus
104. Rifatu Amos
105. Nguba Bura
106. Monica Enoch
107. Sarah Enoch
108. Rifkatu Galang
109. Dorcas Yakubu
110. Deborah Solomon
111. Solomon Pona
112. Saraya Amos
KY KARANTA: Da dumi-dumi: Najeriya ce ta 1 a shigo da kayayyaki daga kasashen waje, WTO
A wani labarin, Ministar Harkokin Mata, Pauline Tallen, ta ce ‘yan matan makarantar Chibok da aka sako suna da kwazo a makarantu kasancewar wasu sun riga sun shiga jami’a wasu kuma sun shirya rubuta jarabawar kammala sakandare (SSCE), The Nation ta ruwaito.
Tallen ta bayyana hakan ne a Abuja a ranar Alhamis a yayin sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) tare da kungiyar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya (IOM), inda ta ce ita da kanta ta ziyarci 'yan matan a makaranta.
Yayin da Masar da Morocco suka shiga sahun masu fitar da kaya a duniya karkashin jagorancin Amurka, Najeriya ta kasance ba a bayyana ta a cikin jerin masu fitar da kayayyakin kasuwanci a duniya ba.
Asali: Legit.ng