An Shiga Tashin Hankali a Sokoto: Ƴan Bindiga Sun Sace Amarya da Wasu Ƙawayenta
- Wasu ‘yan bindiga masu biyayya ga Bello Turji sun sace sabuwar amarya tare da wasu kawayenta hudu a jihar Sokoto
- Lamarin ya faru ne a Kwaren Gamba kusa da Kuka Teke, wani kauye da ya dade yana fuskantar hare-hare daga ‘yan bindiga
- An ce yan bindigar sun yi awon gaba da amaryar da kawayenta da karfin tsiya bayan sanya tsoro a tsakanin mazauna yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sokoto - An shiga matsanancin tashin hankali a karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto yayin da 'yan bindiga suka sace amarya da kawayenta hudu.
An rahoto cewa 'yan bindigar, masu biyayya ga Bello Turji sun farmaki Kwaren Gamba, kusa da kauyen Kuka Teke a jihar ta Sokoto.
'Yan bindiga sun sace amarya da kawayenta
Mai sharhi kan lamuran tsaro, Zagola Makama ne ya sanar da hakan a shafinsa na X, inda ya ce 'yan bindigar sun sace amaryar jim kadan da daura mata aure.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton Zagazola Makama ya nuna cewa 'yan bindigar sun farmaki Kwaren Gamba a ranar Asabar, inda suka yi awon gaba da amaryar da kawayenta hudu.
An ce yankin Kwaren Gamba da ke kuka da Kuka Teke ya sha fama da hare-haren 'yan bindiga masu biyayya ga shugaban 'yan ta'adda Bello Turji.
Mutane na kallo aka tafi da amaryar
Majiyar Zagola ta shaida cewa gungun 'yan bindigar dauke da manyan makamai sun kusa cikin kauyen, inda suka sace amaryar ana tsaka da shagalin biki.
Majiyar ta ce mutane na kallo amma ba su iya tabuka komai ba saboda irin shirin da 'yan bindigar suka yi, dole suka zura ido har aka tafi da amaryar.
Wannan lamari dai ya jefa iyalan amaryar da kawayenta cikin tashin hankali, inda matasa da dattawa suka nuna takaicinsu kan faruwar lamarin.
An sace amarya awanni kafin daura aure
A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun sace wata amarya awanni kafin daura mata aure a jihar Filato.
Wani shaidan gani da ido ya sanar da cewa 'yan bindigar sun shiga har gidan fasto inda amarya za ta kwana kafin a daura aurenta tare da yin awon gaba da ita.
Asali: Legit.ng