Tirkashi: An sace Amarya awanni kafin daura aure a jihar Filato

Tirkashi: An sace Amarya awanni kafin daura aure a jihar Filato

  • Wasu da ba'a gano ko su waye ba sun yi awon gaba da wata mata dake shirin zama Amarya jihar Filato
  • Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa maharan sun farmaki gidan Fasto da dare, inda matar zata kwana kafin ɗaura mata Aure, suka tafi da ita
  • Kakakin yan sandan jihar, ASP Ubah Ogiba, yace akwai yuwuwar ba sace ta aka yi ba, ta tafi gidan wani ne ta kwana

Plateau - Wata budurwa dake shirin zama Amarya, Farmat Paul, ta shiga hannun masu garkuwa da mutane awanni kaɗan kafin ɗaura aurenta a jihar Filato.

Daily Trust tace an sace Amaryan, wacce ke zaune a yankin ƙaramar hukumar Bokkos, jihar Filato, a gidan Fasto, inda ake tsammanin zata kwana kafin a ɗaura mata aure.

Kara karanta wannan

Dan kasuwa ya daba wa matarsa wuka har lahira bayan ya dirka mata saki a Adamawa

Wani shaidan gani da ido ya bayyana wa manema labarai cewa yan bindigan sun farmaki gidan Faston da misalin ƙarfe 10:45 na dare, kuma suka yi awon gaba da Amaryan kaɗai.

Jihar Filato
Tirkashi: An sace Amarya awanni kafin daura aure a jihar Filato Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wata majiya daga cikin iyalan wacce aka sace ta shaida mana cewa an shirya gudanar da ɗaura Auren ne a kauyen Ngyong ranar Lahadi, kamar yadda Tribune ta rahoto.

Shin yan sanda sun samu rahoto?

Da aka tuntubi kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Filato, ASP Ubah Gabriel Ogiba, yace duk ba babu wanda ya kawo musu rahoto, amma sun samu labari, kuma tuni jami'ai suka duƙufa nemanta.

Yace lamarin ka iya yuwu wa ba sace Amaryan aka yi ba, inda ya ƙara da cewa:

"Wata ƙila ba sace ta aka yi ba saboda akwai wani lokaci da wata mata ta tafi gidan wani domin ta kwana amma akai ta yaɗa cewa wasu sun sace ta."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan bindiga sun shiga har gida sun sace matar ɗan uwan kwamishina da ɗansa

"Tun sanda lamarin ya faru babu wanda ya kawo mana rahoto amma a halin yanzu muna gudanar da bincike kan inda ta shiga. Kada mutane su yi gaggawar cewa garkuwa aka yi da ita."

A wani labarin na daban kuma Gwamnan Uzodinma na jam'iyyar APC zai fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci a Jiharsa idan Allah ya kaimu Talata

Kwamishinan yada labarai na jihar Imo, Mista Emelumba, yace gwamna zai bayyana wa mutane sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci

Gwamna Hope Uzodinma na jam'iyyar APC mai mulki ya jima yana ikirarin gwamnatinsa ta gano waɗan nan mutanen dake daukar nauyin ta'addanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel