Zamfara: 'Yan bindiga sun afkawa wasu ƙauyuka bayan kama mahaifin shugabansu 'Turji'

Zamfara: 'Yan bindiga sun afkawa wasu ƙauyuka bayan kama mahaifin shugabansu 'Turji'

  • Yan bindiga masu biyaya ga shugaban yan bindiga Turji sun kai hare-hare wasu kauyuka a Zamfara
  • Hakan ya biyo bayan damke mahaifin Turji da jami'an tsaro suka yi a Kano kimanin makonni biyu da suka gabata
  • Turji ya ce idan har mahaifinsa ba zai yi bikin sallah a gida tare da iyalansa ba toh mutane da dama suma ba za su yi sallah a gidansu ba

Yan bindiga masu biyayya ga hatsabibin ɗan bindigan Zamfara mai suna Turji sun bazama ƙauyuka a ƙaramar hukumar Shinkafi suna sace mutane da matafiya kan kama mahaifin shugaban su.

Sun fara hare-haren ne a ranar Juma'a inda sun sace kimanin mutane 150 a cewar rahoton Daily Trust.

Zamfara: 'Yan bindiga sun afkawa wasu ƙauyuka bayan kama mahaifin shugabansu 'Turji'
Taswirar jihar Zamfara. Hoto: The Punch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: 'Karfin Hali: Ƴan Bindiga Sun Fara Rubutawa Mutane Wasika Kafin Su Kawo Hari a Sokoto

Daliy Trust ta gano cewar jami'an tsaro ne suka kama mahaifin Turji kimanin makonni biyu da suka gabata a Kano kuma har yanzu ba a san inda ya ke ba.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shugaban 'yan fashi ya kai hari kauyukan Zamfara, ya sace mutum 150 saboda an kama mahaifinsa

Ƙauyukan da aka kai wa harin sun hada da Kurya, Keta, Kware, Badarawa, Marisuwa, Maberaya da wasu.

Bayan kai hare-hare a kauyukan, yan bindigan sun kuma sace matafiya da dama a kan hanyar Gusau zuwa Sokoto.

An gano cewa shugaban yan bindigan ya ɗau alƙawarin muddin mahaifinsa ba zai yi sallah a gidan ba wasu mutane da dama suna ba za su yi bikin sallar da iyalansu ba.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Hoton Yadda Aka Yi Jana'izar Janar Na Sojan Nigeria Da Ƴan Bindiga Suka Kashe

"An kira shi a wayar tarho yayin taro tsakanin mutanen gari da jami'an tsaro amma bai zo ba saboda kama mahaifinsa, yana mai cewa shine ɗan ta'addan an kuma san inda ya ke, don haka bai ga dalilin kama mahaifinsa ba," a cewar wata majiya ta da halarci taron.

A cewar wata majiyar daban, Turji ya aike da sakon gargadi da wasu ƙauyukan da 'suke bashi hadin kai' yana faɗa musu su bar gidajensu.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Mai Sanda Mai Daraja Ta Ɗaya, Sun Nemi Maƙuden Kuɗi Na Fansa

Yaransa sun kuma tafi garin Shinkafi a daren ranar Juma'a inda suka sace mata biyar.

Wani mazaunin garin, Mohammed Sani ya shaidawa Daily Trust cewa wani gurneti da aka harba garin ya lalata wasu sassan fadar sarki.

Kakakin yan sandan jihar Zamfara, Mohammed Shehu bai amsa kirar da aka yi masa ba domin ji ta bakinsa.

'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Mai Sanda Mai Daraja Ta Ɗaya, Sun Nemi Maƙuden Kuɗi Na Fansa

A wani labarin, kun ji cewa an yi garkuwa da basarake mai sanda mai daraja ta daya a jihar Kogi, Adogu na Eganyi a karamar hukumar Ajaokuta, Alhaji Mohammed Adembe kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka sace basaraken ne a ranar Talata a kan hanyar Okene zuwa Adogo, rahoton Vanguard.

Sace basaraken na zuwa ne kwanaki uku bayan sace wani kwararren masanin kimiyyan magunguna, AbdulAzeez Obajimoh, shugaban kamfanin magunguna na AZECO Pharmaceutical da ke Ozuwaya a Okene, yankin Kogi Central.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Sace Matar Tsohon Shugaban Karamar Hukuma a Jigawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel