NABTEB Ta Saki Sakamakon Jarabawar 2024, 65% na Dalibai Sun Sami Kiredit 5
- NABTEB ta sanar da cewa dalibai 44,000 daga cikin 67,751 sun sami kiredit biyar da sama da hak a jarrabawar NBC da NTC ta shekarar 2024
- Dakta Nnasia Asanga ya jaddada bukatar samar da kudade da tallafi ga ilimin fasaha domin magance kalubalen da ake fuskanta a fannin
- Duk da an samu koma baya a bana, hukumar NABTEB ta ci gaba da jajircewa wajen haɓaka ilimin fasaha da kuma yaƙi da satar jarrabawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Benin - A wata muhimmiyar sanarwa daga Benin a ranar Alhamis, hukumar jarrabawar NABTEB ta bayyana sakamakon jarrabawar NBC da NTC ta 2024.
Daga cikin dalibai 67,751 da suka zana jarrabawar, 44,000 ne suka samu kiredit biyar da sama da haka, wadanda suka hada da darasin Lissafi da Ingilishi.
NABTEB ta saki sakamakon jarrabawar 2024
Wannan adadi ya nuna kashi 65.35 na jimillar daliban da suka zana jarabawar a bana, inji rahoton jaridar The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dakta Nnasia Ndareke Asanga, magatakardar NABTEB, ya ce dalibai 62,235, kwatankwacin kashi 92.42, sun samu kiredit biyar ko sama da haka, tare da Ingilishi da Lissafi ko ba tare da su ba.
An gudanar da jarrabawar NABTEB ne a cibiyoyi 1,708 da ke a fadin kasar nan.
Dakta Asanga ya bayyana kalubalen da suka shafi ilimin fasaha a Najeriya, da suka hada da yadda masana'antu, kamfanoni, da al'umma ke kallon shirye-shiryen TVET, da kuma karancin kudade da tallafi.
Kalubale da shawarwari kan NATBTEB
Ya kuma jaddada bukatar samar da dokokin da suka dace, da karfafawa malaman ilmin kere-kere, isassun kudi da samar da karin kwalejojin fasaha.
"Shirye shiryen TVET za su samar da mahadar da ake bukata tsakanin ilimi da rashin aikin yi da ita ce makoma a cikin tattalin arziki a yau."
- A cewar Dakta Asanga.
Sai dai ya yi nuni da cewa an samu koma baya a bana idan aka kwatanta da sakamakon shekarar da ta gabata, inda ya bayyana cewa dalibai 349 ne suka yi satar jarabawa.
Rikicin da ya barke a hukumar NABTEB
Idan ba a manta ba, a baya Legit Hausa ta rahoto cewa gwamnatin tarayya ta rusa Majalisar gudanarwar Hukumar jarrabawar nan ta NABTEB kan matsalolin da suka dabaibaye ta.
Tun kafin nan, sai da gwamnatin ta yi kokarin dakatar da shugaban na NABTEB sannan aka tsige wasu manyan Darekotci kafin daga bisani a dawo da wasu bakin aiki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng