Satar jarabawa na cikin abubuwan suka haifar da matsalolin da muke fama dasu a Najeriya, Farfesa Salisu Shehu

Satar jarabawa na cikin abubuwan suka haifar da matsalolin da muke fama dasu a Najeriya, Farfesa Salisu Shehu

  • Farfesa Salisu Shehu, shugaban jami'ar Al-Istiqama ya alakanta matsalar da Najeriya ke ciki da satar jarabawa
  • Fitaccen malamin ya bukaci a koma kan gaskiya in har ana son komai ya gyaru inda yayi misali da gwamnatin Kaduna da ta dauka mataki
  • Ya ce matukar aka cigaba da yaudarar juna ba tare da an tashi tsaye ba, haka matsalolin za su cigaba da yawaita

Kano - Shugaban jami'ar Al-Istiqama da ke Sumaila a jihar Kano, Farfesa Salisu Shehu, ya alakanta matsalolin da kasar nan ke fama da su da satar jarabawa.

Kamar yadda Legit.ng ta zanta da fitaccen malamin, ya yi karin haske kan matsalar magudin jarabawa duba da yadda kullum alkalumman ke hauhawa.

Satar jarabawa na cikin abubuwan suka haifar da matsalolin da muke fama dasu a Najeriya, Farfesa Salisu Shehu
Satar jarabawa na cikin abubuwan suka haifar da matsalolin da muke fama dasu a Najeriya, Farfesa Salisu Shehu. Hoto daga Salisu Shehu
Asali: Facebook

Duk da malamin ya ce bai yi mamakin alkalumman da aka bayyana na wannan shekarar ba, ya ce akwai abubuwan da suke taka rawar gani wurin dauke hankulan dalibai daga karatu.

Kara karanta wannan

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa kan ta tuba, aure ya mutu

Shugaban jami'ar ya ce ba bangare daya kadai za a dora wa laifin wannan matsalar ba, akwai abubuwan da ke bada gudumawa wurin hauhawar yawan masu satar jarabawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Malamin ya ce matukar za a koma wa gaskiya, babu shakka za a samu mafita a kan wannan mummunar dabi'ar da kuma mafita a matsalolin kasar nan.

Malamin ya bukaci a koma kan gaskiya idan ana son ganin gyara a harkar.

Kamar yadda ya ce:

"Yanzu a jihar Kaduna, da gwamna El-Rufai ya so a koma kan gaskiya ba ka ga abinda ya faru ba? Abinda ya faru a jihar Kaduna ba manuniya ba ce?
"Ba jarabawa aka yi wa malamai ba, aka ba su tambayoyi da 'yan firamare ya kamata su amsa suka kasa amsawa alhali kuma su ne malamai da suke koyarwan?

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

"Toh ai wannan shi ne, shugaba ya yadda cewa a fuskanci gaskiya ko zai yi bakin jini domin dama gyara dole sai da bakin jini.
"Amma idan ya zamana za a yi dodorido, a yaudari juna, toh sai a cigaba da tafiya a haka. Ina tabbatar muku da cewa, hatta matsalolin nan na tashe-tashen hankula, satar jarabawa na taka rawar gani."

Sojojin Nijar sun ceci sojin Najeriya da 'yan bindiga suka kai wa farmaki sansaninsu a Sokoto

A wani labari na daban, dakarun sojin kasar Nijar sun ceci sojojin Najeriya 9 wadanda suka tsere yayin da 'yan bindigan daji suka far musu a Sokoto.

Majiyoyi sun sanar da Daily Trust cewa an ceci sojin Najeriyan a Basira, wani kauye da ke kan iyaka karkashin yankin Hodan Roumdji a jamhuriyar Nijar a ranar Juma'a.

Daily Trust ta ruwaito yadda 'yan bindiga suka kai farmaki sansanin hadin guiwa na sojoji da ke sansanin Burkusuma a karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto inda suka kashe jami'an tsaro.

Kara karanta wannan

Jerin mutane 6 da ke da hannu a yawaitar magudin jarrabawa a Arewacin Najeriya, Prof. Salisu Shehu

Asali: Legit.ng

Online view pixel