NABTEB ta fitar da sakamakon jarabawar May/June 2016
– Hukumar Jarabawa ta NABTEB ta fitar da sakamakon Jarabawar May/June ta wannan shekara ta 2016.
– NABTEB ta bayyana cewa fiye da rabin wadanda suka rubuta jarabawar sun samu nasara a shaidar takardar Turanci da lissafi.
– Dalibai har 68,437 suka rubuta wannan jarabawa ta NABTEB wannan shekarar.
Hukumar Jarabawa ta National Business and Technical Examinations Board ‘NABTEB’ ta fitar da sakamakon Jarabawar wannan shekara inda aka bayyana cewa fiye da rabin wadanda suka rubuta sun haye.
A ranar Alhamis dinnan ne 18 ga watan Agusta, Hukumar Jarabawa ta NABTEB ta bayyana cewa ta fitar da sakamakon Jarabawar May/June na shekarar bana, Hukumar ta bada wannan sanarwa ne jiya, a Birnin Benin na Jihar Edo. Shugaban Hukumar ya bayyana cewa cikin daliban da suka rubuta jarabawar a fadin kasar, guda 69, 472, kusan 32, 280 sun samu nasara a takardar Turanci da lissafi. Alkaluman sun nuna kashi kusan 56% suka samu nasara, yayin da kashi 54% ba su samu shaidar Turanci da kuma lissafin ba.
KU KARANTA: NA GANO TAKARDUN MAKARANTA NA-INJI DAN TAKARAR GWAMNAN EDO
Rajistrar Hukumar ta bayyana cewa cikin dalibai 64,437 da suka zauna rubuta jarabawar, akwai kwas-kwasai na harkar zama Injiniya har guda 15, da kuma wasu dabam. Gaba daya dai an zauna zana takardu har 36, wanda ciki akwai guda 16 na gaba-gari. Rajistar wanda itace Shugabar Hukumar Jarabawar ta bayyana cewa na samu matukar cigaba wannan karan, ba kamar a baya ba. Dalibai da dama sun samu nasara a Jarabawar wannan shekarar.
Shugaban Hukumar tayi kira da Gwamnati da ta maida hankali wajen ganin yara dalibai sun koyi sana’o’i, hakan zai taimake su wajen samun saukin rayuwa. Farfesa Isuigo Abanihe ta bada shawarar horar da dalibai, wanda hakan zai kawo cigaba a Kasar gaba daya.
Kwanakin baya ne dai Hukumar Jarabawar WAEC ta saki jarabwar dalibai inda aka nuna cewa kashi 53% sun samu nasara a jarabawar ta WASSCE, sai dai an cewa rike sakamakon dalibai 137,295.
Asali: Legit.ng