Nasarawa: NASIEC Ta Shirya Gudanar da Zaben Ciyamomi, An Fitar da Jadawali
- Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Nasarawa ta ce ta kammala shirye-shiryen gudanar da zaben kananan hukumomi 13
- Shugaban NASIEC, Ayuba Wandai-Usman, ya ce za a gudanar da zaben ciyamomi da na kansilolin a ranar Asabar, 2 ga Nuwamba
- Ayuba Wandai-Usman ya bayyana cewa jam'iyyun siyasa za su fara yakin neman zabe daga ranar Juma’a 18 ga watan Oktoba 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Nasarawa - Hukumar zabe mai zaman kanta ta Nasarawa ta kammala shirye-shiryen gudanar da zaben kananan hukumomi a fadin jihar.
A yayin da Nasarawa ke da kananan hukumomi 13 da kuma sama da mutane miliyan 2.5, hukumar NASIEC ta ce za ta gudanar da zaben a ranar Asabar 2 ga Nuwambar 2024.
Shugaban hukumar NASIEC, Ayuba Wandai-Usman ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Lafiya a ranar Laraba, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a yi zaben ciyamomi a Nasarawa
Zaben dai zai hada da na shugabannin kananan hukumomi (ciyamomi) da na kansiloli.
“Za a gudanar da zaben ciyamomi da na kansiloli a ranar Asabar, 2 ga Nuwamba, 2024.
"Za a gabatar da takardun tsayawa takarar zaben ne a hedikwatar hukumar, Democracy House, titin Shendam da ke garin Lafiya.”
- A cewar Ayuba Wandai-Usman.
An gudanar da zaben kananan hukumomi na karshe a jihar Nasarawa a watan Oktoban 2021, inda zababbun shugabannin za su shafe wa’adin shekaru uku, wanda a yanzu ya zo karshe.
NASIEC: Tsare-tsaren gudanar da zaben
Shugaban NASIEC ya kuma bayyana cewa jam'iyyun siyasa za su fara zaben fitar da gwani da kuma warware takaddamar zaben daga ranar Juma’a 11 ga watan Oktoba 2024.
Ana sa ran jam'iyyun siyasa za su fara yakin neman zaben shugabannin kananan hukumomin da na kansiloli daga ranar Juma’a, 18 ga Oktoba, 2024.
Jaridar New Telegraph ta rahoto cewa za a kuma a fitar da jerin sunayen 'yan takara na ƙarshe a ranar Talata, 29 ga Oktoba, 2024.
Da yake jawabi ga manema labarai, Wandai-Usman ya jaddada kudirin hukumar na hada kai da kafafen yada labarai domin inganta tsarin dimokuradiyya a jihar Nasarawa.
Nasarawa: APC ta lashe kujerun ciyamomi
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Nasarawa (NASIEC), ta sanar da sakamakon zaɓen kananan hukumomi 13 na jihar.
NASIEC ta bayyana cewa jam'iyyar APC mai mulkin jihar ce ta samu nasara a baki ɗaya kujerun ciyamomi 13 da kansiloli 147 da aka gudanar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng