Da Ɗumi-Ɗumi: NABTEB Ta Fitar Da Sakamakon Jarrabawar Nov/Dec 2020

Da Ɗumi-Ɗumi: NABTEB Ta Fitar Da Sakamakon Jarrabawar Nov/Dec 2020

- Sakamakon jarrabawar NABTEB na November/December ta 2020 ta fito

- Ifeoma Isiugo-Abanihe shugaban hukumar na kasa ne ta bada sanarwar

- Isiugo-Abanihe ta ce kashi 92.42% sun samu kredit biyar da fiye da haka

Rajistara kuma shugaban hukumar shirya jarrabawa na NABTEB, Farfesa Ifeoma Isiugo-Abanihe ta sanar da cewa sakamakon jarrabawar da aka rubuta a watannin Nuwamba da Disamba na bara sun fito, rahiton The Nation.

Ta bayyana cewa kashi 75.72 cikin jimillar dalibai 21,175 da suka zana jarrabawar sun sama kredit biyar da abin da ya fi haka ciki har da darrusan Ingilishi da lissafi, yayin da kashi 92.42 cikin 100 wato dalibai 25,844 sun samu kredit biyar da lissafi da Ingilishi da wanda ba su da shi.

Yanzu-Yanzu: NABTEB Ta Fitar da Sakamakon Jarrabawar Nov/Dec 2020
Yanzu-Yanzu: NABTEB Ta Fitar da Sakamakon Jarrabawar Nov/Dec 2020. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Isiugo-Abanihe ta bayyana hakan ne a jiya a hedkwatar hukumar na kasa da ke Benin a lokacin da ta ke sanar da sakamakon jarrabawar tare da sauran manyan jami'an hukumar.

KU KARANTA: Wani Mutum Ya Kutsa Wurin Casu Ya Bindige Mutum 6 Ciki Har da Budurwarsa

Ta yi kira a mayar da hankali kan ilimin fasaha da sana'i'i (TVET) a dukkan matakai a kasar tana mai cewa ilimin TVET din ne zai shirya matasa da manyan mutane a kasar su samu sana'o'in da za su iya dogara da kansu.

Isiugo-Abanihe ta ce duk da kallubalen annobar korona da ta janyo jinkiri wurin rubuta jarrabawar May/June da November/December, NABTEB ta yi nasarar yin dukkan jarrabawan biyu daga baya.

Ta ce hukumar za ta cigaba da gudanar da jarrabawa masu inganci a kowane shekara sannan za ta cigaba da inganta tsarin yin jarrabawar don magance magudi.

KU KARANTA: An Kama Hatsabibin Ɗan Shekara 30 Da Ke Yi Wa Mutane Fyaɗe a Sokoto

Ta ce, "A jarrabawar da ya fito, dalibai 250 wato kashi 0.77 cikin 100 ne aka samu da laifin magudin zabe.

"Wannan cigaba ne idan aka kwatanta da dalibai 603 wato kashi 1.23 cikin 100 na daliban da suka rubuta jarrabawar November/December 2019 da aka samu da laifin magudin jarrabawa."

Isiugo-Abanihe ta ce za a cigaba da yin rajistar jarrabawar NABTEB NBC/NTC har zuwa karshen watan Mayu.

A wani labarin daban tsohon mataimakin shugaban kasa Mr Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da musgunawa kafafen watsa labarai da yi wa yan kasa barazana idan sun bayyana ra'ayoyinsu.

Atiku ya yi wannan zargin ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter @atiku domin bikin ranar Yan Jarida na Duniya.

Ya bayyana cewa idan ana tauye hakkin mutane a mulkin demokradiyya, hakan zai kawo rashin jituwa tsakanin mutane da gwamnatin kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164