Rikicin Hukumar NABTEB: Na yi kokarin fadawa Minista Adamu Adamu gaskiya amma bai yiwu ba - Leonard Shilgba
- Kwanaki Majalisar gudunarwar NABTEB ta tsige Shugaban Hukumar jarrabawar
- Sai dai kuma Gwamnatin Buhari ta dawo da Shugaban da wasun sa bakin aikin su
- Shugaban Majalisar gudanarwar NABTEB ya zargin Ministan ilmi da danne gaskiya
Ku na sane cewa a cikin ‘yan kwanakin nan ne Gwamnatin Tarayya ta rusa Majalisar gudanarwar Hukumar jarrabawar nan ta NABTEB. Kafin nan dama an yi kokarin dakatar da shugaban na NABTEB sannan aka tsige wasu manyan Darekotci.
Sai dai yanzu mun ji labari cewa Shugaban gudanarwan Mista Leonard Shilgba na zargin Ministan ilmi na kasar Mallam Adamu Adamu da kokarin yin rufa-rufa kan wasu abubuwa na ba dai-dai ba a Hukumar da ma Ma’ikatar ilmi na Najeriya.
KU KARANTA: Tirsasa Buhari aka yi ya sa hannu kan kasafin bana - Sumaila
Jaridar Premium Times tace Leonard Shilgba ya fitar da jawabi ne na musamman bayan an rusa Majalisar gudanarwar hukumar. Shilgba yace yayi kokarin ganawa da Ministan ilmi domin fayyace masa barnar da ake yi amma abin ya ci tura.
Leonard Shilgba yace akwai wata barna da ake yi a Hukumar jarrabawar Kasar don haka su kayi bincike su ka tsige Shugaban Hukumar da wasu da aka kama da laifi. Sai dai Gwamnati ta dawo da wadanda aka kora bakin aiki sannan ta rusa Majalisar.
A makon nan ne mu ka samu labari cewa tashar bisar da aka kaddamar farkon shekarar nan a Jihar Kaduna ta jawowa Najeriya makudan kudin da su ka haura sama da Naira Biliyan 2.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng