Rana Ta Baci: Mai Maganin Gargajiya Ya Kashe Mutum Wajen Gwajin Maganin Bindiga

Rana Ta Baci: Mai Maganin Gargajiya Ya Kashe Mutum Wajen Gwajin Maganin Bindiga

  • Jami’an rundunar ‘yan sandan Edo sun kama wani malamin tsibbu mai shekaru 19 da haihuwa bisa zargin ya kashe wani mutumi
  • Rahotanni sun ce malamin tsibbun ya harbe mutumin har lahira a lokacin da suke gwajin maganin bindiga da ya hadawa mamacin
  • Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Moses Yamu, ya ce mai ba da maganin zai fuskanci hukunci da zarar an kammala bincike

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Edo – Jami’an ‘yan sanda sun kama wani mai ba da maganin gargajiya bisa zargin kashe wani mutumi Alex Ezekiel, a lokacin da ya ke gwajin maganin bindigar da ya hada masa.

An tattaro cewa matashin malamin tsibbun ya yi kaurun suna a wajen shirya maganin da zai hana harsashin bindiga ko kuma karfe ya kama jikin mutum.

Kara karanta wannan

An shiga jimami a Kano, gini ya danne mata da 'ya'yanta ana tsaka da tafka ruwan sama

'Yan sanda sun yi magana kan bokan da ya kashe wani mutumi garin gwajin maganin bindiga
Edo: Mai maganin gargajiya ya kashe wani mutumi garin gwajin maganin bindiga.
Asali: Original

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Moses Yamu, ya ce lamarin ya faru ne a unguwar Onumu da ke Akoko-Edo a Edo, a ranar 20 ga Agusta, inji rahoton The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

SP Yamu ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 2 ga Satumba

Maganin harsashin bindiga ya ki aiki

Kamar yadda PM News ta ruwaito, kakakin 'yan sandan ya kara da cewa wanda aka kashe ne ya tuntubi mai ba da tsarin domin ya shirya masa maganin hana harsashi ya kama shi.

“Bayan shirya maganin, malamin tsibbun ya yi kokarin gwada ingancinsa ta hanyar harbin marigayin da bindiga.
"Abin bakin ciki, marigayin ya samu munanan raunuka kuma an garzaya da shi asibitin Ifejola, Igarra, inda likita ya tabbatar da mutuwarsa."

- A cewar SP Yamu.

Duba wasu labarai kan maganin bindiga:

Kara karanta wannan

Harin ƴan bindiga ya fusata gwamna, za a sake buɗe sansanin sojoji a Arewa

Maganin bindiga: An kashe matashi

A wani labarin, mun ruwaito cewa an cafke wani mai sayar da maganin gargajiya, Usman Saidu, bisa laifin salwantar da rayuwar wani matashi dan shekara 27 a jihar Katsina.

An gano cewa marigayin ya mutu ne bayan ya sayi maganin bindiga daga hannun Usman Saidu wanda ya tabbatar masa cewa babu wani harsashi da zai iya ratsa jikinsa idan ya sha.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.