Dan Najeriya Ya Bindige Mahaifinsa Har Lahira a Garin Gwada Maganin Bindiga
- Wani uba ya mutu a hannun dansa a garin gwada maganin bindigan da aka ba shi a wani yankin jihar Adamawa
- Rahoton da muka samo na 'yan sanda ya bayyana cewa, a halin yanzu dan yana tsare, ana ci gaba da bincike don gano gaskiya
- Ana yawan samun mutanen da ke shiga hadari domin karbar maganin bindiga ko wani makamancin haka
Jada, jihar Adamawa - Wani dan Najeriya, Yusuf Adamu ya hallaka a hannun agolansa da ya umarta ya gwada ingancin maganin bindigan da aka ba shi a jihar Adamawa, Daily Trust ta ruwaito.
Adamu, an ce ya umarci agolan nasa mai suna Suugbomsumen Adamu ne ya gwada harba bindigar a kansa don gwada ingancin sabon maganin da ya samu da yake kyautata zaton zai kare shi daga harsashi.
An ruwaito cewa, mutumin ya ci fariyar cewa, yanzu dai ya samu kariya tunda ya karbo maganin bindigan, don haka ya umarci agolan ya harbe shi.
Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi a kauyen Sankipo a karamar hukumar Jada ta jihar Adamawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan sanda sun yi bayanin halin da ake ciki
A cewar rahoton 'yan sanda, dan da ya yi harbin har yanzu yana hannun 'yan sanda, Sahara Reporters ta ruwaito.
Da yake tabbatar da lamarin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Adamawa, SP Suleiman Nguroje ya ce:
"Mutumin da ya yi harbin yana tsare.
"'Yan sanda za su binciki lamarin a tsanake sannan su tabbatar an yi adalci, ba tare da la'akari da dangartakan da ke tsakanin mamacin da wanda ya yi harbin ba."
Nguroje ya kuma shawarci al'umma da su guji amfani da wani magani da sunan zai kare su daga harsashin bindiga, kana ya umarce su da su kasance masu bin doka da oda don zama lafiya da kuma kare kansu daga halaka.
Wa ya kashe kaninsa da sunan gwada maganin bindiga
A labari maikama da wannan, wani matashi mai suna Abubakar ABubakar ya bindige dan uwansa da sunan gwada maganin bindiga.
Mamacin Yusuf Abubakar da dan uwansa 'ya'yan wani mafarauci ne a jihar Kwara, kuma sun gwada ingancin maganinsu na gado ne.
Rahoton majiya ya bayyana cewa, yanzu dai an tsare wanda ya yi harbin a hannun 'yan sanda don ci gaba da bincike.
Asali: Legit.ng