Ajali ko Ganganci? Matashi Ya Bindige Kaninsa Yayin Gwajin Layar Maganin Bindiga

Ajali ko Ganganci? Matashi Ya Bindige Kaninsa Yayin Gwajin Layar Maganin Bindiga

  • Matashi ya bindige kaninsa mai shekaru 12 yayin da yake gwada layar maganin bindiga da ya karbo Kwara
  • Kamar yadda aka gano, Abubakar ya dauko bindigar tokar mahaifinsa wanda mafarauci ne kuma ya saita kaninsa tare da gwada layar a kansa
  • A take Yusuf ya fadi yace ga garinku yayin da Abubakar ya cika bujensa da iska amma ‘yan sanda sun bazama bincike da nemansa

Wani matashi mai suna Abubakar Abubakar ya bindiga kaninsa mai suna Yusuf Abubakar mai shekaru 12 har lahira yayin da yake gwada aikin sanuwar layar maganin bindigarsa.

Abubakar da mamacin duk ‘ya’yan wani mafarauci ne a karamar hukumar Kaiama dake jihar Kwara, Daily Trust ta rahoto hakan.

Taswirar Kwara
Ajali ko Ganganci? Matashi Ya Bindige Kaninsa Yayin Gwajin Layar Maganin Bindiga. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Lamarin kamar yadda aka tattaro, ya faru a ranar Lahadi kuma Abubakar har yanzu bai shiga hannun hukuma ba don ya tsere bayan aikata laifin.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar PDP Za Ta Kira Taron Gaggawa Domin Ceton Takarar Atiku Daga Watsewa

A yayin magana kan faruwar lamarin a ranar Litinin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, Okasanmi Ajayi, yace kwamishinan ‘yan sanda Paul Odama, ya bukaci bincike kan lamarin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Bayan kare kansu da layar, babban ‘dan ya fito da bindigar tokar mahaifinsa kuma ya bindige ‘dan uwansa. Layar bata yi aiki ba kuma Yusuf yace ga garinku a take.”

- Okasanmi yace.

Channels TV ta rahoto, Okasanmi ya shawarci iyaye da masu kula da yara da su kiyaye dukkan al’amuran ‘ya’yansu.

“Su kasance masu kiyaye dukkan abubuwa marasa kyau domin gujewa faruwar irin wannan lamarin.”

- Yace.

Ohanaeze Ndigbo Sun yi wa Atiku Martani Kan Ikirarin Zai Mikawa Ibo Shugabancin Kasa

A wani labari na daban, kungiyar kololuwa ta kabilar Ibo, Ohanaeze Ndigbo a jiya ta zakulo maganar da ‘dan takarar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar yayi inda yake ikirarin cewa shi ne zai kasance tsanin da zai kai Ibo shugabancin kasa inda suka kwatanta batun da abin dariya.

Kara karanta wannan

Duk Yaudara Ce: 'Yan Najeriya Sun Yi Martani Ga Bidiyon Atiku Na Tika Rawa Da Na Tinubu Na Tuka Keke

A cikin kwanakin nan ne Atiku ya ziyarci Enugu inda ya hana da manyan masu ruwa da tsakin yankin tare da cewa shugabancin kasa na kabilar Ibo zai zo ne daga wurin shi bayan ya kammala wa’adin mulkinsa, jaridar Guardian ta rahoto.

Ya jaddada cewa, dukkan zabukan da aka yi a yanar gizo sun bayyana cewa Obi ne ke dauke da nasara ba wai a matsayinsa na ‘dan takarar shugaban kasa na Ibo ba, sai dai matsayin mai hada kan dukkan yankunan kasar nan.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel