Yadda mai maganin gargajiya ya rasa ransa wajen gwajin maganin bindiga
Chinaka Adoezuwe, mai maganin gargagiya dan shekaru 26 a duniya ya gamu da ajalinsa yayin da ya umurci wani daga cikin wanda ya zo wurinsa neman maganin bindiga, Chukwudi Ijezie, ya gwada harbinsa don tabbatar da cewa maganin na aiki.
Lamarin ya faru ne a kauyen Umuozu Igiri da ke karamar hukumar Isial Mbano dake Jihar Imo.
Wani mazaunin kauyen mai suna Kingsley Ugochukwu ya shaidawa Punch cewa Ijezie wanda yanzu yana hannun yan sanda ya tafi wajen mai maganin ne don ayi masa maganin da zai hana harsashi ratsa jikinsa.
KU KARANTA: 'Yan sanda sun kama shugaban 'yan fashin da yaransa suka dakatar dashi a Kano
Rahotanni sunce bayan da Adoezuwe ya kammala hada maganin ya umurci Ijezie ya tsaya don ya harbe shi don a gwada maganin amma yaki amincewa da hakan. Saboda ya yarda da maganin da ya hada, Adoezuwe sai ya umurci Ijezie ya harbe shi.
Daga nan ne fa Ijezie ya amince ya harbi Adoezuwe kuma hakan ya yi sanadiyyar rasuwarsa.
A lokacinda yake tabbatar da afkuwar lamarin, Kakakin hukumar yan sanda, Andrew Enwerem ya ce jami'an hukumar sun kama wanda ake zargi da kisan kuma yana tsare.
Enwerem ya ce, "Wanda ake tuhuma yana hannun mu, wannan kisar gilla ce. Jami'an yan sanda reshen Isial Mbano sun kama shi saboda a tabbatar da tsaro a unguwar."
"Za'a mayar da binciken zuwa ga sashin masu binciken manyan laifuka na Owerri saboda sun cigaba da gudanar da bincike," inji Enwerem.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng