Magani na Gagarar Talaka: Masu Ciwon Sukari Sun Nemi Alfarma Wajen Shugaba Tinubu

Magani na Gagarar Talaka: Masu Ciwon Sukari Sun Nemi Alfarma Wajen Shugaba Tinubu

  • Masu fama da ciwon sukari a Najeriya sun roki Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya sanya tallafi a magunguna da abinci
  • Ko’odinetan kungiyar mutane masu fama da sukari na kasa, Bernard Enyia ya ce talauci ya sa sun koma shan maganin gargajiya
  • A cewar Bernard Enyia, allurar insulin da a 2022 suke sayenta a kan N4,000 yanzu ta koma tsakanin N19,000 zuwa N24,000

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Calabar - Farashin da ake sayar da allurar da ake yiwa masu ciwon sukari ta yi tashin gwauron zabi, lamarin da ya jefa masu fama da lalurar a damuwa.

Kungiyar masu fama da ciwon sukari ta kasa ta roki gwamnatin tarayya da ta sanya tallafi a farashin magunguna da kayan abinci.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Ministan Tinubu ya fadi yadda Najeriya za ta shawo kan karancin abinci

Masu fama da ciwon sukari sun yi magana kan tsadar magunguna da abinci
Masu fama da ciwon sukari a Najeriya na neman daukin Tinubu. Hoto: Wavebreakmedia
Asali: Getty Images

Ko’odinetan kungiyar na kasa, Bernard Enyia, ya yi wannan roko a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Calabar ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matsin tattali ya shafi magunguna

Mista Enyia ya ce masu fama da ciwon sukari na fuskantar mawuyacin hali, saboda tsadar magunguna da kayan abinci.

Ya nuna damuwarsa kan yadda kalubalen tattalin arzikin da ake fama da shi ya kara tabarbarewar halin da suke ciki tare da zama silar mutuwar marasa lafiya.

Mista Enyia, ya kuma bayyana cewa yawancin masu fama da ciwon sukari sun koma amfani da magungunan gargajiya saboda tsadar na asibiti, inji rahoton Premium Times.

"Magunguna sun yi tsada" - Enyia

A cewar Mista Enyia:

“Farashin kayan abinci da kayan masarufi, gami da magungunan ceton masu ciwon sukari sun yi tashin gwauron zabi.
"Wannan ya sa ya zama babban kalubale ga masu ciwon sukari su iya sayen magungunansu na yau da kullun."

Kara karanta wannan

Sunayen gwamnonin Arewa da ake zargin sun kitsa zanga zangar adawa da Tinubu, Rahoto

Ya ba da misali da allurar insulin da a cewarsa, a shekarar 2022 ake sayar da ita a kan N4,000 amma a yanzu tana tsakanin N19,000 zuwa N24,000.

An nemi alfarmar Tinubu

Bayan zayyana irin kalubale da masu fama da ciwon sukari suke fuskanta a kasar, kodinetan kungiyar ya roki Shugaba Bola Tinubu da ya sanya tallafi a magunguna.

Ya bayyana cewa umarnin da Shugaba Bola Tinubu ya ba da na baya-bayan nan da nufin saukake shigo da abinci da kayayyakin magunguna bai yi tasiri ba.

Ya ce matakin bai rage musu halin da suke ciki ba.

“Ba a samar da magungunan ciwon sukari a Najeriya, haka nan ana shigo da injinan da ake amfani da su wajen gwajin sukarin daga kasashen waje."

- A cewar Enyia.

Ciwon sukari na damun Obasanjo

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ce tsawon shekaru 35 ciwon sukari na addabar rayuwarsa.

Obasanjo ya ja hankalin yara da matasa da su kula da cutar sukari matuka ta hanyar kiyaye salon rayuwa, yana mai cewa ciwon sukari na da matukar hadari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.