Obasanjo: Shekaru 35 ciwon suga na azabtar dani ba kakkautawa, amma ban mutu ba

Obasanjo: Shekaru 35 ciwon suga na azabtar dani ba kakkautawa, amma ban mutu ba

  • Tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bayyana yadda ciwon suga ya wahala shi
  • A cewwarsa, ya dauke shi shekaru 35 yana fama da ciwon suga, amma har yanzu yana nan karau
  • Shugaban ya kuma bayya matakan da ya dauka suka taimakeshi wajen sarrafa ciwon na suga

Abeokuta - Tsohon shugaban kasan Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya ba bayyana siriin yadda ya ke lallaba rayuwarsa da ciwon suga a shekaru 35 da suka gabata, yayin da ya ce ciwon ya kashe abokan sa da dama amma shi gashi nan garau, Daily Nigerian ta ruwaito.

Cif Olusegun Obasanjo ya fede biri har wutsiya kan batun a ranar Laraba 18 ga watan Agusta a wani bikin da ya halarta na rufe taron ci gaban yara masu ciwon suga na jihar Ogun da aka gudanar a Abeokuta ta jihar ta Ogun.

Kara karanta wannan

Taliban: Ba ma gaba da kowa, mun yafe wa duk wadanda suka yake mu a baya

Taron wanda Cibiyar Ciwon suga ta Talabi ta shirya, ya koyar da yara 21 da ke fama da ciwon suga mataki na 1 a jihar kan yadda ake fama da cutar.

A wani rahoto da Daily Trust ta rahoto, Obasanjo ya ja hankali da kuma shawartar yara da su kula da cutar suga matuka ta hanyar kiyaye salon rayuwa, yana mai cewa ciwon suga ba cuta ne da bai kai wa ga halaka.

Obasanjo: Shekaru 35 ciwon suga na azabtar dani ba kakkautawa
Tsohon shugaban kasan Najeriya, Obasanjo | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Tsohon shugaban ya zayyana wa yaran cewa, lallai su guji shan suga da ma abinci mai dauke da sinadarin carbohydrate sananna a kullum su tabbatar sun rika yin alluran insulin domin kula da cutar da kyau sosai.

Jawabin da Obasanjo ya yi

A wani yanki na jawabin da ya yayi, ya ce:

Kara karanta wannan

Gidan Soja: Dalilin da yasa muke karbar tuban mayakan Boko Haram da suka mika wuya

“An gano ina dauke da ciwon suga sama da shekaru 35 kenan kuma ga ni nan garau, har yanzu ina tafiya, har yanzu ina tsalle-tsalle sama da kasa, har yanzu ina yin abubuwa da yawa mutane da yawa a shekaruna ba za su iya ba.
"Daga lokacin da aka gano ina dauke da ciwon suga, da dama cikin abokaina sun rasu kuma dalilin kenan ba sa kula da ciwon suga yadda ya kamata su kula shi ba.
“Ba komai ko don mutan mataki na daya ne ko kuma na biyu ba, ya zuwa yanzu babu maganin ciwon suga, watakila za a sami magani kafin in mutu, amma ina addu’ar a sami magani kafin ku mutu.

Obasanjo: Kara yawa da al'ummar Afrika ke yi na hana ni bacci cikin dare

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya ce karuwar yawan mutanen Afirka na fuskantar mummunan yanayi, yanayin da ya ce, yana hana shi bacci cikin dare.

Kara karanta wannan

Tsadar abinci: Dalilin da yasa 'yan Najeriya za su ci gaba da cin bakar wahala, in ji masana

Jaridar The Cable ta rahoto cewa Obasanjo yayi wannan tsokaci ne a ranar Talata, 17 ga watan Agusta lokacin da yake magana yayin gabatar da rahoton sabuwar kungiyar cigaban Afrika (APG).

Da yake bayyana tsoronsa ga yawan karuwar mutane, Obasanjo ya ce:

“Tambayoyi guda uku suna tasowa a raina a duk lokacin da tunanin ban tsoro na yawan mutanen da ke karuwa ya hana ni rintsawa da dare. Tambaya ta farko ita ce: ta yaya za mu ciyar da wannan yawan mutane masu haihawa? ”

Jaridar Daily Sun ta rawaito cewa Obasanjo yayi magana da karfin sa a wurin taron a matsayin shugaban APG.

Komai ya dawo daidai: Shugaba Buhari zai fito daga kullen Korona ranar Laraba mai zuwa

A wani labarin, A ranar Laraba ne Shugaba Muhammadu Buhari zai fito daga killacewar da ya shiga tun bayan dawowarsa daga Landan ranar Juma’a da ta gabata, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Kara karanta wannan

A tura 'yan Boko Haram da suka tuba zuwa gonaki, tsohon Janar ya shawarci FG

A bisa ka'ida, dole ne ya killace kansa a matsayin matakin taka tsantsan da ake bukata daga duk matafiya na duniya da ke shigowa Najeriya domin rage yaduwar Korona.

Wasu daga cikin ma’aikatan Babban Kwamishinan Najeriya a Burtaniya wadanda ake tunanin sun kasance tare da shugaban an ce sun kamu da cutar. Amma ba a san ko sun taba kasancewa kusa da shi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel