Lafiya jari: Alamomin cutar sukari guda bakwai

Lafiya jari: Alamomin cutar sukari guda bakwai

Cutar sukari (diabetes) faruwa ne sakamakon yawan sindarin glucose (sukari) a jinin dan adam kuma cutar da kasu kashi uku ne akwai nau'i na 1 da na 2 sannan akwai cutar sukarin masu dauke da juna biyu.

Sai dai a halin yanzu ciwon sukarin nau'i na 2 shine yafi yaduwa cikin al'umma kuma wasu abubuwan da ke asassa samuwarsa sun hada da kiba, rashin motsa jiki, yawan shekaru, rashin cin abinci mai kyau da kuma kwayoyin halitar gado.

Rahoton da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta fitar ya nuna cewa adadin wadda cutar zai hallaka nan da shekaru 10 zai dara wanda ke mutuwa yanzu da 50% saboda galibin mutane ba su kulawa da alamominta har zai ya tsananta.

Duk da cewa cutar bata cika bayyana lokaci guda ba, Hukumar Lafiyar ta Duniya ta wallafa wasu alamomi da mutane za su rika lura da su wadda za su iya taimakawa wajen kiyaye kamuwa da cutar ko kuma takaita illar da za ta yiwa mutum.

Alamomin cutar sukari guda bakwai
Alamomin cutar sukari guda bakwai
Asali: Depositphotos

Ga alamomi bakwai da ya dace mutane su rika lura da su:

1. Yawan fitsari (Polyuria)

Yawan fitsari ba tare da wani dalili na musamman ba yana daga cikin alamun ciwon sukari. Wannan yana faruwa ne saboda kodar mutum bata iya rika sukari da yawa saboda haka sai ta bari sukarin ya hade da fitsari idan zai kara janyo ruwan jikin mutum sai su fita ta fitsari.

2. Jin kishin ruwa ko da yaushe

Yawan kishin ruwa shima yana daga cikin alamun ciwon sukari saboda yawan sukarin da ke jinin mutum zai rika jin kishin ruwa sosai kuma gashi yana fitar da ruwan ta hanyar fitsari saboda haka babu wuya an sake jin kishin ruwan.

DUBA WANNAN: Jihohi 10 da suka fi bunkasa a Najeriya a yanzu

3. Jin yunwa ko da yaushe

Yawan jin yunwa yana daga cikin alamomin farko na ciwon sukari. Hakan na faruwa ne saboda tsokar jikin mai ciwon bata iya amfani da sukarin da ke jikinsa wurin samar da kuzari saboda rashin sinadarin insulin, wannan kuma zai saka mutum ya rika bukatar karin abinci.

4. Rashin warkewar ciwo da wuri

Akwai dalilai da dama da ke sanya ciwo ya ki warkewa da wuri amma ciwon sukari na daya daga cikinsu. Saboda haka idan ka lura ciwo ko yanka baya saurin warkewa a jikinka, yana da kyau ka ziyarci likita.

5. Rashin gani sosai

Rashin gani sosai yakan samu mutanen da ba su kulawa da ciwon sukari. Alama ce da ke nuna sukari ya yi yawa a jikin mutum ana da zarar sukarin ya dawo daidai idanun sai su washe.

6. Ramewa ba tare da wani dalili ba

Idan mutum ya lura yana ta ramewa babu wani sananen sabibi, yana da kyau da tafi wurin kwaruru a duba sukarinsa domin shima alama ce na ciwon sukarin.

7. Tabbai a fatar mutum

Daya daga cikin alamun farko na cutar sukari shine fitowar tabbai musamman a wuyan mutum, da hammata da matsematsinsa. A turence ana kiransa Acanthosis nigricans.

Daga karshe idan mutum ya lura yana fama da wasu alamomi da muka lissafa a nan sai ya garzaya ya tuntubi likita domin ayi masa gwaji tare tare da bayar da shawarwari da suka dace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel