Karin kumallo da kwoi yana taimakon masu ciwon suga –Bincike

Karin kumallo da kwoi yana taimakon masu ciwon suga –Bincike

-A maimakon yin karin kumallo da hatsi, kwoi yakamata masu ciwon suga su rinka karyawa dashi a cewar Farfesa Little

-Ciwon suga yana da alaka da sinidarin insulin wanda idan babu shi isasshe toh tabbas matsala zata auku ta ciwon suga

Duk da cewa yawancin mutane sunfi karkata zuwa ga hatsi domin kari, sai dai wani Farfesa ya shawarci masu fama da ciwon suga da su rinka amfani da wani abin na daban.

Farfesa Jonathan Little wanda ke koyarwa a Jami’ar Burtaniya ta Kwalombiya (UBC) a sashen lafiya da motsa jiki shine ya wallafa wata takarda inda yake nunin cewa abinci mai kitse sosai da kuma karanci sinadarin carbohydrate yana taimakama masu ciwon suga.

Karin kumallo da kwoi yana taimakon masu ciwon suga –Bincike
Karin kumallo da kwoi yana taimakon masu ciwon suga –Bincike
Asali: UGC

KU KARANTA:Jagorancin majalisar dattawa: ‘Yan najeriya zasu samu kyakkyawan jagoranci daga wurina, inji Lawan

“ Akasarin abinda ke biyo bayan karin kumallo musamman ga masu ciwon suga ya kasance saboda rashin nagartar sinadarin insulin. Kuma idan muka lura zamu ga mutane musamman na yammacin duniya sunfi karyawa da hatsi wanda ke kunshe da carbohydrate mai yawan gaske.” Inji Little.

Karin kumallo na matukar haifar da matsala musamman ga masu fama da ciwon suga. Bincikensa ya nuna mana cewa cin abinci mai kitse da yawa fiye da carbohydrate shine mafi kyawon yin kari da safe. Yin hakan zai rage matsalolin da suka shafi ciwon suga (Diabetes).

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng