Gwamnati Ta Saki Hotuna da Bayanan Fursunonin da Suka Tsere Daga Gidan Yarin Suleja
- Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar kula da gidajen gyaran hali ta saki bayanan fursunonin da suka tsere daga gidan yarin Suleja
- Hukumar NCoS ta ce ta zabi bayyana bayanan fursunonin ne domin ganin an kamo su tare da mayar da su gidan yarin cikin gaggawa
- Sanarwar ta roki 'yan Najeriya da su tuntubi hukumar NCoS ta lambar waya ko adireshin imel da zarar sun ga daya daga cikin fursunonin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Makonni 11 bayan da fursunoni 69 suka tsere daga gidan gyaran hali na Suleja a jihar Neja, a karshe gwamnatin tarayya ta bayyana hotuna da bayanan su.
Hukumar da ke kula da gidajen gyaran hali na Najeriya (NCoS) ta bayyana cewa an dauki matakin ne a kokarin ganowa, kamowa da kuma dawo da wadanda suka tseren.
An saki bayanan fursunonin da suka tsere
Abubakar Umar, mai magana da yawun hukumar gidajen gyaran halin ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar kuma aka wallafa a shafin NCoS na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abubakar ya bayyana cewa sai da aka yi doguwar tattaunawa tsakanin hukumomin da abin ya shafa kafin aka wallafa sunaye, hotuna, da bayanan fursunonin.
A cewarsa, hakan zai ba sauran jami'an tsaro da ma 'yan Najeriya damar sa ido domin gano fursunonin da suka tsere wanda zai taimaka wajen mayar da su gidan yarin.
Gwamnati ta dauki matakan kama fursunonin
Sanarwar ta roki 'yan Najeriya da su ba hukumar NCoS hadin kai wajen ganin an kama fursunonin da suka tsere domin dakile matsalar tsaro da shigarsu jama'a ka iya haifarwa.
Ta kara da cewa hukumar ta dauki matakai na sintiri da na leken asiri a kokarin ganin an sake cafke fursunonin, yayin da ta ta ce an dauki mataki a sauran gidajen gyaran hali na kasar.
A cewar sanarwar:
“Idan aka ga daya daga cikin wadanda suka tsere, jama’a za su iya kai rahoto ga jami’in tsaro ko hukuma mafi kusa ko kuma su iya kiran lambobi kamar haka: 07087086005, 09060004598, ko 08075050006."
"Jama'a kuma na iya tuntuɓar mu ta adireshinmu na imel akan: info@corrections.gov.ng ko complainsresponsedesk@corrections.gov.ng"
Duba sunaye, hotuna da bayan fursunonin a nan kasa:
Suleja: Fursunoni sun tsere daga gidan yari
Tun da fari, mun ruwaito cewa kusan fursunoni 119 ne suka tsere a gidan gyaran hali da ke Suleja a jihar Neja a daren Laraba 24 ga Afrilu, 2024.
Fursunonin sun tsere ne bayan rugujewar katangar da ta kewaye da gidan yarin sakamakon mamakon ruwan sama a ranar Larabar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng