Gwamnatin tarayya ta saki hotunan Fursunonin da suka gudu a Jos

Gwamnatin tarayya ta saki hotunan Fursunonin da suka gudu a Jos

  • An kaddamar da yunkurin damko fursunonin da suka gudu daga gidan yarin Jos, jihar Plateau
  • Hukumar gidajen gyara hali NCoS ta yi kira ga yan Najeriya su taimaki hukuma wajen damkosu
  • An kaddamar da bincike don sanin matsalar da aka samu suka gudu

Hukumar gidajen gyara hali a ranar Juma'a, 9 ga Yuli, ta saki hotunan fursunonin da suka gudu daga Kurkukun da ke Jos, birnin jihar Plateau.

Hukumar ta bayyana hotunan a shafinta na Facebook mai taken: Fuskokin fursunonin da suka gudu daga gidan yarin Jos.

An shawarci yan Najeriya da ke da labari kan inda za'a gano wadannan mutane su tuntubi ofishin yan sanda mafi kusa.

KU DUBA: Magoya bayan Buhari ba za su taba barin Tinubu ya zama Shugaban Kasa ba – Lamido

Gwamnatin tarayya ta saki hotunan Fursunonin da suka gudu a Jos ranar Alhmis
Gwamnatin tarayya ta saki hotunan Fursunonin da suka gudu a Jos Hoto: Nigerian Correctional Service
Asali: Facebook

DUBA NAN: Mune kurar baya a kowane bangare, kuma ba mu da ilimi: A cewar wata ‘yar Arewa cikin bidiyo

Kara karanta wannan

Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Turo Mana Bidiyon Yadda Suka Aurar Da Ƴaƴanmu Mata, Iyayen Ɗaliban Kebbi

Yadda suka gudu

Kontrolan yankin, Samuel Aguda, ya bayyana yadda suka gudu daga gidn yarin.

Aguda ya ce sakacin jami'an dake tsare fursunonin ne ya haifar da hakan.

Yace:

"Lokacin da nazo wajen. Na lura cewa ko dai sun samu kofin makullin gidan yari ne ko kuma sakaci daga bangaren jami'ai."
"Ta katanga suka arce."

Ya kara da cewa mutum hudun na tsare ne gabanin gurfanar su a kotu kan laifin garkuwa da mutane da fashi da makami.

Gwamnatin tarayya ta saki hotunan Fursunonin da suka gudu a Jos
Gwamnatin tarayya ta saki hotunan Fursunonin da suka gudu a Jos Hoto: Nigerian Correctional Service
Asali: Facebook

Makiyaya ne suka gudu

Wata majiya ta bayyanawa manema labarai cewa wadannan fursunoni da ake zargin makiyaya ne sun gudu daga gidan yarin ne cikin daren Alhamis, 8 ga Yuli.

The Nation ta kara da cewa makiyayan da suka gudu sun gurfana gaban kotun majistare dake karamar hukumar Barkin Ladi a shekarar 2020.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng