Zanga-zangar EndSARS: Obaseki ya ba fursunonin da suka tsere nan da Juma'a su koma

Zanga-zangar EndSARS: Obaseki ya ba fursunonin da suka tsere nan da Juma'a su koma

- Gwama Godwin Obaseki ya bayar da wa'adin Juma'a, 23 ga waatan Oktoba, ga fursunonin da suka tsere a jihar Edo

- Fursunoni 1,993 ne suka gudu bayan wasu yan iska sun fasa gidan gyaran halayya biyu a jihar yayin zanga-zangar EndSARS

- Zuwa yanzu dai guda 163 sun shiga hannu, inda shida suka mika kansu da kansu

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya ba fursunonin da suka tsere daga gidan gyara hali na Benin dake hanyar Sapele da na Oko zuwa Juma’a, 23 ga watan Oktoba, su mika kansu ko kuma su fuskanci tsattsauran hukunci.

Gwamnan ya bayar da wa’adin kwanaki ukun ne a Benin, a ranar Laraba, 21 ga watan Oktoba, yayinda yake rangadin duba wuraren da aka bata yayin zanga-zanga.

Shugaban gidan gyaran halayyar reshen jihar Edo, Babayo Maisanda, ya sanar da cewa shida daga cikin fursunoni 1,993 da suka tsere a yayinda aka fasa kurkukun sun dawo da kansu.

A tuna cewa wasu yan iska da suka kwace ragamar zanga-zangar lumana na EndSARS a jihar ne suka kai hari gidajen yarin a ranar Litinin.

KU KARANTA KUMA: Shugaban ƙasa 2023: Jerin sunayen mutane 5 da PDP ta fitar, ɗaya zai gaji Buhari

Zanga-zangar EndSARS: Obaseki ya ba fursunonin da suka tsere nan da Juma'a su koma
Zanga-zangar EndSARS: Obaseki ya ba fursunonin da suka tsere nan da Juma'a su koma Hoto: Leadership
Asali: UGC

Sun kuma saki fursunonin da ke gidajen yarin bayan sun farfasa ginin tare da kaiwa ma’aikatan wajen hari.

Mai sanda ya sanar da cewa an sake kama fursunoni 163, yayinda shida daga ciki suka mika kansu sannan kuma cewa har yanzu ba a samu sauran 1,818 ba.

Gwamna Obaseki wanda ya nuna dimuwa a kan irin barnar da aka yi yayinda ya je rangadin ya samu rakiyar mataimakinsa, Philip Shaibu, wani mataimakin Sufeto Janar na yan sanda, Celestine Okoye.

Har ila yau, kwamishinan yan sanda, Johnson Kokumo, wakilan rundunar sojojin Najeriya na sama da kasa, rundunar NDCDC da na FRSC duk sun kasance a wajen.

Obaseki ya yi korafi a kan tarin barnar da aka yi, inda ya kara da cewa hakan ya saba ma kudirin masu zanga-zangar EndSARS na akika wadanda suka gudanar da gangaminsu cikin lumana.

KU KARANTA KUMA: Shiru magana ce, caccakata a yanar gizo ba mafita bace - Fatima Ganduje-Ajimobi

Ya sha alwashin cewa ba zai zauna ya zubawa yan iska ido suna aikata irin haka ba, ya kuma yi watsi da harin da aka kaiwa jami’an tsaro.

Sannan ya gargadi fursunonin da su mika kansu a ofishin yan sandan jihar Edo, birnin Benin don mayar da su gidan gyara halin, Nigerian Tribune ta ruwaito.

“Tir da irin wannan barna kuma mun san masu zanga-zangar #EndSARS za su taya mu yin Allawadai da wannan aika-aika da bata-gari suka yi.

“Mun ba wa fursunonin da suka tsere zuwa ranar Juma’a su dawo hedikwatar ’yan sanda ko su fuskacin hukunci mai tsanani idan hukuma ta cafke su”, inji Obaseki

Ya kara da cewa: "Wadanda basu dawo ba bayan daren Juma'a, muna da rikodinsu dukka, muna da bayanasu, za mu bibiyesu sannan mu tabbatar da mun dawo da su da kuma yanke masu hukuncin da ya dace."

A gefe guda, Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers ya bayyana cewa an saka dokar ta baci awa 24 a wasu daga cikin kananan hukumomin jihar saboda yadda ƴan tada kayar baya suke kawo ruɗani a zanga zangar #ENDSARS a jahar.

Dokar za ta yi aiki ne a kananan hukomomin Oyigbo da kuma wani bangare na kananan hukumomin Obio-Akpor da Port Harcourt.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel