Gwamnatin tarayya ta saki hotuna da sunayen Fursunonin da suka gudu a Owerri
- Hukumar gidajen gyara halin Najeriya ta nuna alamun ta shirya damke fursunonin da suka gudu da gidan garin Owerri
- Hukumar na kira ga jama'a su taimaka wajen tona asirin duk wanda suka gani cikinsu
- Har yanzu mutum guda aka kama cikin wadanda suka tsere daga gidan yari
Sakamakon ballewa daga gidan yarin garin Owerri, jihar Imo da wasi fursunoni sukayi, hukumar gidajen gyara halin Najeriya ta sake hotuna da sunayen fursunonin da suka gudu.
Hukumar NCS a ranar Juma'a, 9 ga Afrilu, ta shafinta na Tuwita, ya saki hotunan wasu da sunayen fursunonin.
Kawo yanzu, an saki hotunan fursunoni 45.
Legit.ng ta kawo muku yadda wasu yan bindiga suka balla gidan yarin Owerri ranar 5 ga Afrilu kuma suka saki Fursunoni 1,884.
Amma kawo ranar Alhamis, 78 cikin fursunonin sun koma da kansu.
DUBA NAN: Soja ya karyata ikirarin cewa an kashe mutum 70 a Binuwai 3
KU KARANTA: A nuna mana gawawwakinsu: Soja ya karyata ikirarin cewa an kashe mutum 70 a Binuwai
Ministan harkokin cikin gida, Rauf AregbeSola ya yi kira ga Fursunonin da suka gudu daga gidan yarin Owerri cewa su dawo da kansu.
Ministan ya yi alkawarin cewa duk Fursunan da ya dawo, za'a yafe masa kura-kuransa.
Aregbesola ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyara ta musamman gidan yarin a ranar Talata biyo bayan harin da yan ta'addan IPOB suka kai.
Asali: Legit.ng