Kamfanin BUA Zai Gina Katafaren Asibitin Zamani Kyauta a Jihar Arewa

Kamfanin BUA Zai Gina Katafaren Asibitin Zamani Kyauta a Jihar Arewa

  • Mai kamfanin BUA, Abdulsamad Rabi'u ya dauki kudurin samar da katafaren asibitin zamani ga jami'an kwastam a Bauchi
  • A jiya Litinin ne aka daura tubalin ginin asibitin inda ya samu halartar manyan jami'an gwamnati da al'ummar yankin
  • Shugaban hukumar kwastam, Adewale Adeniyi ya bayyana jin dadin hukumar kan yadda Abdulsamad Rabi'u ya tuna da su

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - A jiya Litinin, 8 ga watan Yuli aka daura tubalin ginin asibitin hukumar kwastam a jihar Bauchi dake Arewa maso gabas.

Rahotanni sun nuna cewa mai kamfanin BUA, Alhaji Abdulsamad Rabi'u ne ya dauki nauyin ginin katafaren asibitin.

Kara karanta wannan

An samu karin mutanen da suka mutu a harin bam da aka kai jihar Borno

Hukumar Kwastam
Abdulsamad Rabi'u ya kaddamar da gina asibiti a Bauchi. Hoto: NIgeria Customs Service.
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanan ne a cikin wani sako da hukumar kwastam ta wallafa a shafinta na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Girman asibitin BUA a Bauchi

Shugaban hukumar kwastam na kasa, Adewale Adeniyi ya tabbatar da cewa asibitin zai kasance mai girman gado 30 ne.

Adewale Adeniyi ya bayyana cewa za a gina asibitin ne a tsarin zamani tare da samar da kayan aiki domin lura da marasa lafiya.

Kwastam ta yi godiya ga BUA

A yayin daura tubalin ginin, hukumar kwastam ta ce lallai Alhaji Abdulsamad Rabi'u ya yi abin kirki wajen samar da asibitin.

Adewale Adeniyi ya ce tabbas asibitin zai taimaka wajen kiyaye lafiyar jami'an kwastam da al'ummar yankin da aka gina asibitin.

Amfanin asibitin BUA ga al'umma

Wanda ya wakilci al'ummar yankin yayin bikin daura tubalin, Tanko Dutse ya yi godiya bisa kawo asibitin jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

Ina aka kai maƙudan kuɗin da aka ƙwato daga ɓarayin ƙasa a mulkin Buhari?

Tanko Dutse ya bayyana cewa daukacin al'ummar jihar Bauchi za su samu fa'ida wajen inganta lafiyarsu daga asibitin.

Za a gina asibitin 'yan majalisu

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya bayyana cewa a wannan shekarar za a ginawa 'yan majalisar tarayya katafaren asibiti.

Sanata Akpabio ya bayyana cewa sanatoci, 'yan majalisar wakilai, ma'aikata da baƙi ne za a riƙa dubawa a cikin asibitin idan an gina shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng