Gina katafaren Asibiti: Dankwambo ya sha yabo daga bakin Osinbajo

Gina katafaren Asibiti: Dankwambo ya sha yabo daga bakin Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jinjina tare da yaba ma gwamnan jahar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo bisa wani muhimmin aiki da yayi na gina katafaren asibitin Mata da kananan yara a jahar.

Legit.ng ta ruwaito Osinbajo ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 27 ga watan Mayu yayin da yake kaddamar da katafaren asibitin mai cin gadaje 250 wanda zai kula da Mata da kananan yara a jahar Gombe.

KU KARANTA; Tafiyar Singham: Kalli sabon kwamishinan Yansanda da aka tura Kano

A jawabinsa, Osinbajo ya bayyana cewa samar da asibitin zai taimaka wajen shawo kan matsalolin da ake fama dasu a sha’anin kiwon lafiya a jahar. “Shugaban kasa Buhari na son irin wannan aiki, kuma ya sha nanata muhimmancin kiwon lafiya ga cigaban Najeriya.

“Don haka nake cike da farin ciki a yau game da wannan katafaren asibiti da gwamnatin Dankwambo ta gina, kuma ya zama dole a jinjina masa.” Inji shi.

Da yake nasa jawabin, kwamishinan kiwon lafiya na jahar, Dakta Kennedy Ishaya yace dalilin gina wannan asibiti shine kasancewar ana yawan samun mutuwar mata masu juna biyu da jariransu a yankin Arewa maso gabas, don haka aka samar da asibitin don shawo kan wanna matsalar.

Bugu da kari Osinbajo ya kaddamar da makarantar sakandari ta Hassan Model School wanda gwamnatin Dankwambo ta gina a garin Gombe akan kudi naira miliyan 736, inda kwamishinan ilimi na jahar, Abdullahi Isiaku yace tun a shekarar 1924 turawa suka gina makarantar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng