Gwamnatin Tarayya Za Ta Canja Matsugunnin Wasu Gidajen Gyaran Hali, Ta Fadi Dalili

Gwamnatin Tarayya Za Ta Canja Matsugunnin Wasu Gidajen Gyaran Hali, Ta Fadi Dalili

  • Olubunmi Tunji-Ojo, ministan harkokin cikin gida ya ce za a sauyawa wasu gidajen yari matsugunni a Najeriya
  • Ministan ya ce ka'idar doka ita ce a yi su inda ke da nisan mita akalla 100 daga jama'a, amma yanzu gidaje na kewaye da garururuwa
  • Matsayin gwamnati mai bin doka, dole ne gyara hakan ta hanyar dauke su zuwa inda babu jama'a saboda tsaro, inji tunji-Oljo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Legas - Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce gwamnatin tarayya tana duba yiwuwar canzawa wasu gidajen gyaran hali matsugunni.

Gwamnatin tarayyar za ta dauke su daga yankunan biranen da suke a halin yanzu.

Ministan Tinubu ya yi magana kan kusancin gidajen gyaran hali da jama'a.
Gwamnatin tarayya na shirin canja matsugunnin wasu gidajen yarin Najeriya. Hoto: @BTOofficial
Asali: Facebook

Ministan ya ce za a yi haka ne saboda yadda birane ke karuwa a zagayensu a maimakon rashin jama'a da ya dace a ce an gani a irin wuraren, jaridar Premium Times ta bayyana.

Kara karanta wannan

"Tuna halacci ke hana ni ɗaukar wasu matakai": Gwamna ga mai gidansa

Misalan da ministan ya bayar sun hada da yanayin yadda gidajen gyaran hali na Suleja da Ikoyi ke ciki, da kuma yadda hakan ke haifar da matsalar tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Gidajen yari sun yi kusa da jama'a" - Minista

Olubunmi Tunji-Ojo ya bayyana rashin dacewar gidan yarin Ikoyi da ke jihar Legas a inda yake yanzu, inda ya ce za a iya samun kalubalen tsaro.

"Tabbas kana iya ganin kotun majistare daga nan, majami'a, gidajen zama, da sauran lamurran kasuwanci duka na kusa da gidan gyara halin
"Gwamnati na duba yadda za ta iya canzawa wasu gidajen gyaran hali matsugunni, kuma gidan yarin Ikoyi na a gaba gaba.
"Kada ku manta doka ta ce a samar da gidan gyara hali inda babu jama'a, akalla nisan mita 100. Kamar yadda kuke gani, yanzu ba haka bane.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta samu bashin $150bn da halatta auren jinsi a yarjejeniyar Samoa?

- A cewar Tunji-Ojo.

Abin da ya faru a gidan yarin Suleja

Jaridar The Cable ta ruwaito Ministan ya kuma buga misali da gidan gyaran hali na Suleja inda ya koka da cewa mita 7 ke tsakaninsa da gidajen jama'a.

Ministan ya kara da cewa, burin gwamnatin Bola Tinubu ne ta mayar da gidajen yari wurin ilimantarwa da gyara tarbiya wadanda suka tsinci kansu a ciki.

Sai dai, ya ce da wuya a iya cimma irin wadannan burukan matukar suna halin da suke ciki a yanzu, inda ya ce gwamnati na bincike domin rage cunkoso a gidajen gyaran halin.

Karo 15 da 'yan bindiga suka balle gidajen yari

A wani labari na daban, mun ruwaito yadda wasu miyagun 'yan bindiga suka balle wasu gidajen gyaran hali a sassa daban daban na Najeriya.

Wadannan lamurran sun faru ne a jihohi daban-daban da suka hada da Edo, Ondo, Legas, Abia, Delta, Imo da sauransu, wanda ya yi silar tserewar wasu fursunoni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.