Jihar Adada: Muhimman Abubuwa 5 Game da Shirin Kirkirar Sabuwar Jiha a Kudu Maso Gabas

Jihar Adada: Muhimman Abubuwa 5 Game da Shirin Kirkirar Sabuwar Jiha a Kudu Maso Gabas

Kudurin kafa jihar Adada ya tsallake karatun farko a majalisar dattawa a ranar Talata, 2 ga watan Yuli. Majalisar wakilai ta kuma tattauna batun kirkirar jihar Etiti a yankin Kudu maso Gabas.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sanata Okey Ezea (LP, Enugu ta Arewa) ne ya gabatar da kudurin mai taken “Kudurin yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin Najeriya, 1999 a shekarar 2024 (SB. 482.)

Sanata Okey ya nemi a gyara sashe na 3 (1) da kuma jadawalin farko, Sashi na 1 na kundin tsarin mulkin Najeriya domin ba da damar sanya sabuwar jihar a cikin doka.

Abin da ya kamata ku sani game da sabuwar jihar Adada da ake shirin kirkira
Kudurin dokar kirkirar sabuwar jiha a Kudu maso Gabas ya tsallake karatu na 1 a majalisar dattawa. Hoto: @SPNigeria
Asali: Facebook

Jihar da ake son a kafa za ta kunshi gundumar Enugu ta Arewa, kuma garin Nsukka ne zai zama babban birnin jihar na Adada idan an kirkireta.

Kara karanta wannan

An gabatar da ƙudirin ƙirkiro ƙarin jiha 1 a majalisar wakilai, ya tsallake karatu na farko

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da haka, akwai wasu manyan abubuwan da ya kamata ku sani game da shirin kafa jihar Adada a yankin Kudu maso Gabas, kamar yadda rahoton Daily Trust ya nuna.

1. Yaushe aka fara batun kirkirar jihar Adada?

Yunusa Kaltungo, dan majalisar tarayya daga jihar Bauchi, ya fara gabatar da kudurin kirkirar jihar Adada a shekarar 1983, inda ya ba da hujjar rashin daidaito wajen raba jihohin kasar.

An kuma sake gabatar da bukatar a gaban kwamitin Mbanefo wanda ya duba yiwuwar samar da karin jihohi, kananan hukumomin jihohi da kuma daidaiton iyakoki a shekarar 1996.

Mutane da dama sun amince da samar da jihar Adada a yayin wani taro a 2005, wanda aka gudanar a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Shekaru uku da suka gabata, jaridar This Day ta ruwaito tsohon shugaban Ohanaeze Ndigbo, Cif John Nnia Nwodo ya nemi majalisar dattawa da ta duba batun kirkirar jihar Adada.

Kara karanta wannan

NIN: Majalisar dattawa na kokarin kawo dokar da za ta shafi yan ƙasashen waje

2. Kirƙirar jihar Adada zai kawo daidaito?

Samar da jihar Adada zai tabbatar da samun daidaiton wakilci da kuma magance rashin daidaiton da aka dade ana fama da shi a rabon jihohin kasar nan.

Domin kuwa a halin yanzu yankin Kudu maso Gabas na da jihohi biyar, idan aka kwatanta da sauran yankuna, wadanda ke da jihohi shida.

3. Menene karfin tattalin arzikin jihar Adada?

Adada tana da ƙasar noman rogo, dawa, da shinkafa. Bugu da kari, yankin yana da arzikin mai da iskar gas, wanda zai iya samar da kudaden shiga da haifar da ci gaban tattalin arziki.

Babban birnin jihar, Nsukka, ita ce karamar hukuma mafi tsufa kuma mafi girma a Najeriya. Ta yi aiki a matsayin hedikwatar gundumomi a lokacin mulkin mallaka.

4. Akwai damarmakin yawon shakatawa a Adada?

Jihar Adada da aka ke son kirkira na da abubuwan jan hankali, kamar tafkuna, da magudanan ruwa na tsaunuka. Wannan zai jawo kudin shiga daga masu yawon bude ido.

Kara karanta wannan

Sokoto: Halin da ake ciki bayan fara sauraron ra'ayin jama'a kan dokar masarautu

Yankin gida ne ga abubuwan jan hankali na halitta da yawa, gami da kyakkyawan tsaunin Nsukka, tsaunin Udenu, da tsaunin Aku.

Masu yawon bude ido za su iya samun kyakkyawan karimcin mutanen Adada ta hanyar ziyartar bukukuwan gargajiya kamar bikin al'adun Nsukka na shekara-shekara.

5. Jihar Adada na da goyon bayan siyasa?

Gwamnatin jihar Enugu da kuma majalisar dokokin jihar Enugu sun nuna goyon bayansu ga kafa jihar Adada. Wannan goyon bayan yana da matukar muhimmanci a siyasance.

Sabanin sauran bukatu na samar da jihohi a Najeriya, jihar Adada na samun goyon bayan siyasa daga jihar Enugu inda ake sa ran fitar da sabuwar jihar daga cikinta.

Majalisa ta yi maraba da jihar Adada

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugabannin majalisar tarayya sun yi maraba da batun kirkirar sabuwar jiha a shiyyar Kudu maso Gabas.

Majalisar tarayya ta bayyana hakan ne a yayin wata ziyara da Cif John Nnia Nwodo da tawagarsa suka kai majalisar tarayyar ne a ranar Laraba, 9 ga watan Fubrairu, 2021.

Kara karanta wannan

"A koma salon mulkinsu Sardauna": An fadawa Tinubu hanyar magance matsalolin Najeriya

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel