Shugabannin Majalisar Tarayya za su goyi bayan a ba Ibo sabuwar Jiha a Kudancin Najeriya

Shugabannin Majalisar Tarayya za su goyi bayan a ba Ibo sabuwar Jiha a Kudancin Najeriya

- John Nwodo ya dawo da maganar kirkiro sabuwar jiha a yankin Kudu maso gabas

- Nwodo da tawagarsa sun je Majalisa, su na neman goyon baya a kafa jihar Adada

- Shugabannin Majalisa sun karbi maganar da hannu biyu-biyu, sun ce za su duba

Tsohon shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo, John Nwodo, ya jagoranci tawaga zuwa majalisar tarayya, su na neman a kirkiro masu sabuwar jiha.

The Cable ta ce Cif John Nwodo da mutanensa su na so a fito da wata jiha da za a kira jihar Adada, daga cikin bangaren Enugu a yankin Kudu maso yamma.

Jaridar ta ce wannan tawaga ta kai ziyara zuwa majalisar tarayyar ne a ranar Laraba, 9 ga watan Fubrairu, 2021, inda su ka gana da shugabannin majalisar.

John Nwodo ya zauna da shugaban majaliar dattawa, Ahmad Lawan, da mataimakinsa, Ovie Omo-Agege, da kuma Femi Gbajabiamila, da Idris Wase.

KU KARANTA: Jigon PDP, Femi Fani-Kayode ya yi karin haske game da shirin sauya-sheka

Ya ce fafutukar neman jihar Adada ta fita dabam saboda babu wanda yake adawa da neman jihar a Enugu ko a wajen jihar, kuma duk Ibo sun karbi maganar.

Idan an yi na’am da wannan jiha, zai zama akwai jihohi uku ta bangaren Arewacin kasar Inyamurai kamar yadda ake da jihohi uku daga shiyyar Kudu.

A ganawar da aka yi da shugabannin majalisar a lokuta dabam-dabam, an shaida wa Nwodo cewa babu wanda yake adawa da wannan jiha da su ke nema.

Lawan ya yi na’am da bukatar da masu fafutukar su ke yi, ya ce majalisa za ta saurari kukansu.

Inyamurai sun tafi Majalisa, sun bukaci a kirkiro masu wata Jiha mai suna ‘Adada’
John Nnia Nwodo Hoto: www.dailypost.com
Asali: UGC

KU KARANTA: ‘Yan Majalisa sun fadi hanyoyin da za a bi a kawo karshen rashin tsaro

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Omo-Agege ya yi maraba da wannan yunkuri, ce za su duba maganar kirkiro wannan sabuwar jiha ta Adada.

A baya mun kawo maku rahoto cewa tsohon shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta mutanen Ibo, John Nnia Nwodo, ya koka a kan nadin hafsun sojojin kasa.

Cif John Nnia Nwodo, ya yi tir da Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari na ware mutanen kasar Ibo a mukaman da ya bada a gidan sojan Najeriya.

Ita ma kungiyar Afenifere ta ce nadin da aka yi jiya ya sake nuna son kan Muhammadu Buhari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel