Jihohi 5 da suka fi sauran yawan albarkatun man fetur a Najeriya

Jihohi 5 da suka fi sauran yawan albarkatun man fetur a Najeriya

An gano man fetur a Najeriya ne a karon farko a shekarar 1956 a garin Oloibiri da ke yankin Neja Delta bayan an kwashe kimanin shekaru 50 ana gudanar da bincike.

A halin yanzu, Najeriya na samar da kimanin gangan man fetur miliyan 2.8 a kowanne rana a kididigar da akayi a 2006 wanda yakan ya dora Najeriya a matsayin kasar da ke kan gaban wajen samar da man fetur a nahiyar Afirka kuma na 6 a duniya.

Jihohi 5 da suke sama wajen albarkatun man fetur a Najeriya
Jihohi 5 da suke sama wajen albarkatun man fetur a Najeriya

Fanin man fetur ne ke samar da 14% na tattalin arzikin Najeriya.

Bayan haka ga jerin jihohin da suka kan gaba wajen samar da man fetur din da adadin abinda suka samarwa wa.

1) Akwa Ibom

Jihar Akwa Ibom ne kan gaba wajen samar da danyen man fetur a Najeriya, jihar tana samar da 31.4% na adadin danyen man fetur da kasar ke samar wa a kowanne rana. Babban birnin jihar itace Uyo kuma anyi hasashen cewa tana daya daga cikin birane masu kyau a Najeriya.

Jihar na da yawan al'umma kimanin miliyan 5 da ke zaune a kananan hukumomi 31 da ke jihar. Manyan kabilai uku da suka fi yawa a jihar sune Oron, Annang da Ibibio.

KU KARANTA: Wata kungiyar Yarabawa ta kwance wa Obasanjo zani a kasuwa

2) Delta

Delta ita ke biye wa Akwa Ibom wajen samar da danyen man fetur inda ta ke samar da 21% na danyen man fetur din da kasar da samarwa. Akwai matatan man fetur da masan'antar sarrafa man a garin Warri. Jihar na da kananan hukumomi 25 da yawan mutane da suka kai miliyan 4. Kabilun da suka fi yawa sune Urhobo, Isokoa da Itsekiri.

3) Rivers

A baya jihar Rivers ita ce kan gaba wajen samar da man fetur din kafin Akwa Ibom ta doke ta. Jihar Rivers ita tafi kowanne jihar tace danyen man fetur a halin yanzu. Jihar na samar da 21.43% na danyen man da Najeriya ke tunkaho dashi. Jihar na da adadin mutane sama da miliyan 5. Kabilun da ke jihar sun hada da Ikwerre, Okrika, Upoho, kalabari, Ubani da sauransu.

4) Bayelsa

Jihar Bayelsa na daya daga cikin jihohin da ke kan gaba wajen samar da man fetur inda jihar ke samar da 18.07% na danyen man fetur a kasar. Garin Oloibiri inda nan ne aka fara gano man fetur mai yawa a shekarar 1959 yana jihar Bayelsa ne. Jihar na da kananan hukumomi 8 da mutanen da yawan su bai dara miliyan 1.9 ba. Manyan kabilun da ke jihar sun hada da Ogbia, Nembe, Izon, da Epie-Atissa.

5) Ondo

Jihar Ondo ce ta biyar a jerin jihohin da ke kan gaba wajen samar da danyen man fetur a Najeriya inda ta ke samar da 3.74% na man da kasar ke samarwa. Jihar Ondo ce kawai jihar da ta fito daga yankin Kudu maso yamma a cikin jerin jihohin da ke samar da man. Jihar na da yawan mutane kimanin miliyan 2.4 da kananan hukumomi 19.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel