Mutuwar Alkalin Babbar Kotun Najeriya Ya Jawo Tsaiko a Tarin Shari’o’i, an Samu Bayanai
- Mutuwar alkalin babbar kotun jihar Oyo, Adegboye Gbolagunte ya jawo ba a saurari shari'ar kowa ba a jiya Talata, 26 ga watan Yuni
- An ruwaito cewa Mai shari'a Adegboye ya rasu ne a ranar Litinin bayan fama da gajeriyar jinya, kuma ya rasu yana da shekara 64
- An ce gandirebobin gidajen gyara hali na jihar sun koma da fursunonin da suka kawo kotun wadanda ke fuskantar shari'a daban-daban
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ibadan, Oyo - Rahotannin da muka samu na nuni da cewa alkalin babbar kotun jihar Oyo, Mai shari'a Adegboye Gbolagunte ya rigamu gidan gaskiya.
Daya daga cikin 'ya'yan marigayin, Oladiran Adegboye ne ya fitar da sanarwar mutuwar alkalin, wanda ya ce ya rasu a ranar Litinin.
Alkalin babbar kotun Oyo ya rasu
Sanarwar ta ce Mai shari'a Adegboye, wanda har zuwa lokacin mutuwarsa shi ne alkalin Babbar kotun Oyo, ya mutu ne bayan gajeriyar jinya, i ji rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta kara da cewa Mai shari'a Adegboye ya mutu yana da shekara 64 a duniya, kuma ya bar mata daya, 'ya'ya uku da jikoki hudu.
Mutuwar alkalin ta tsayar da zaman kotu
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa mutuwar Mai shari'a Adegboye ta kawo tsaiko a shari'o'in da ake yi a mafi faɗin jihar Oyo a ranar Talata.
Sakamakon mutuwar alkalin, dukkanin wadanda suka halarci kotun domin a saurari shari'arsu sun koma gida domin ba a bude kotunan ba.
An ce jami'an hukumar gidajen yari na jihar su ma sun koma da fursunonin da suka kawo kotun da ke jiran a yanke masu hukunci kan laifuffuka daban daban da ake zargin sun aikata.
'Yan ta'adda sun kashe sojojin Nijar 21
A wani labarin, mun ruwaito cewa sojojin kasar Nijar sun fada komar 'yan ta'adda a Tassia Sun Badjo, yankin Yammacin Tillaberi, inda aka kashe sojoji 21.
Gwamnatin kasar Nijar ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku a wata sanarwa da ta fitar a kafar talabijin ta kasar a ranar Talata, 25 ga watan Yuni.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng