Yanzu-yanzu: Alkali Abdul Kafarati ya rigamu gidan gaskiya

Yanzu-yanzu: Alkali Abdul Kafarati ya rigamu gidan gaskiya

Tsohon Antoni Janar na jihar Bauchi kuma Alkalin babban kotun tarayya, Abdul Kafarati, ya rigamu gidan gaskiya.

Majiya daga gidan mamacin ta bayyana cewa Alkalin ya mutu ne bayan Sallar Magariba ranar Alhamis.

A cewar majiyar, Za'a yi masa Sallar Jana'izar a ranar Juma'a a babban Masallacin tarayya dake Abuja bayan Sallar Juma'a.

"Innalillahi Wa inna ilaihi Rajiun. Ina alhinin sanar da mutuwar daya daga cikin dattawansa, Alkali Abdul Kafarati da daren nan bayan Sallan magariba a Abuja," cewar majiyar.

Gabanin rasuwar, Alkali Abdul Kafarati ya kasance tsohon shugaban Alkalan babban kotun tarayya.

Alkalin ya yi ritaya ranar 25 ga Yuli, 2019.

Yanzu-yanzu: Alkali Abdul Kafarati ya rigamu gidan gaskiya
Yanzu-yanzu: Alkali Abdul Kafarati ya rigamu gidan gaskiya
Source: UGC

Source: Legit.ng

Online view pixel