Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Sanatan PDP da Ake Tuhuma da Buga Takardar NYSC Ta Bogi

Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Sanatan PDP da Ake Tuhuma da Buga Takardar NYSC Ta Bogi

  • Mai shari'a Christopher Oba na babbar kotun Birnin tarayya Abuja, ya sallami Sanata Benson Konbowei daga tuhumar buga takardun bogi
  • A watan Maris din 2024 ne gwamnatin tarayya ta yi ƙarar Sanata Konbwei tare da wasu bisa zargin suna amfani da takardun NYSC na jabu
  • Lauya mai shigar da kara, Reuben Egwuaba ya shaidawa kotun cewa ministan shari'a ne ya bukaci a janye tuhumar da ake yi wa sanatan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wata babbar kotu da ke birnin tarayya Abuja ta sallami shari'ar da ake yi tsakanin gwamnatin tarayya da sanatan Bayelsa ta tsakiya, Benson Konbowei .

An gurfanar da Sanata Konbowei na jam'iyyar PDP tare da wasu mutane bisa zargin su da yin amfani da takardun kammala bautar ƙasa (NYSC) na bogi.

Kara karanta wannan

Matsin rayuwa: Tinubu ya shawarci 'yan Najeriya kan yadda za su samu abinci cikin sauki

Kotu ta yi hukunci kan sanatan PDP da ake zargin ya buga takardun bogi
Sanatan PDP, Benson Konbwei, daga jihar Bayelsa. Hoto: Hon. Konbowei Benson
Asali: Facebook

Kotu ta soke tuhumar sanatan PDP

Mai shari'a Christopher Oba ya sallami Konbowei tare da soke tuhumar da ake yi masa jim kadan bayan lauyan da ke karar, Reuben Egwuaba ya nemi ayi hakan, inji rahoton Channels.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Barista Egwuaba ya shaidawa kotun cewa Antoni Janar na tarayya kuma ministan shari'a, Lateef Fagbemi, wanda ya sa aka shigar da karar, yanzu ya nemi a janye gaba daya.

Barista Egwuaba ya gabatar da bukata a gaban kotun na ta sallami sanatan da kuma rushe tuhumar, bukatar da lauyan wanda ake karar bai yi jayayya a kai ba.

Sai dai jaridar The Nation ta ruwaito cewa Mai shari'a Oba, wanda ya sallami Sanata Konbowei , bai karbi korafin lauyan wanda ake kara ba na a soke batun zargin gaba daya.

"El-Rufai ya mallaki gida a Dubai" - Rahoto

Kara karanta wannan

Sanusi II Vs Aminu: Lauya ya fadawa Abba yadda zai kawo karshen rikicin sarautar Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tawagar jaridu 70 karkashin OCCRP sun gano cewa Nasir El-Rufai ya mallaki gidan $193,084 a birnin Dubai.

Abin mamaki, shekara daya kafin fitar da wannan rahoton, tsohon gwamnan na Kaduna ya yi rantsuwa da Allah cewa bai mallaki wani gida a wajen Najeriya ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.