Sanusi II: “Abin da Ya Hana Ni Zuwa Kotu Bayan Ganduje Ya Tsige Ni Daga Sarkin Kano”

Sanusi II: “Abin da Ya Hana Ni Zuwa Kotu Bayan Ganduje Ya Tsige Ni Daga Sarkin Kano”

  • Muhammadu Sanusi II ya bayyana dalilin da ya sa bai yi karar Abdullahi Ganduje ba a lokacin da aka fara tsige shi daga sarkin Kano a 2020
  • Sanusi II wanda Gwamna Abba Yusuf ya mayar da shi kan kujerarsa ya ce bai je kotu ba ba saboda ba zai ji dadin yin aiki da Ganduje ba
  • Sarkin Kano ya bayyana hakan ne bayan da wata kotu ta soke batun tsige abokin hamayyarsa, Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin

Jihar Kano - Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya bayyana ainihin dalilin da ya sa bai kalubalanci tsige shi a matsayin sarki da Abdullahi Umar Ganduje ya yi.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Abba Kabir ya magantu kan mutuncin Aminu Ado, ya fadi masu zuga shi

Mun ruwaito tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya tsige Sanusi II daga kujerar sarki a watan Maris 2020 saboda yawan sabanin da suke samu.

Sanusi II ya yi magana kan tsige shi da Ganduje ya yi a 2020
Sarkin Kano Sanusi II tare da tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje na APC. Hoto: Abdullahi Umar Ganduje, sanusilamidoofficial
Asali: Facebook

Sanusi II: "Ganduje zai kuntata rayuwata"

A wata hira da jaridar The Sun a ranar Asabar, 22 ga Yuni, Sanusi II ya ce yana daya daga cikin daruruwan 'ya'yan sarki a masarautar don haka ba zai ce lallai sai shi kadai zai zama sarki ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito, Sanusi ya bayyana cewa ko da a ce ya je kotu kuma kotu ta mayar da shi, ba zai iya yin aiki da gwamnatin Gwamna Ganduje ba.

Sanusi II, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa bai kalubalanci tsige shi ba a 2020, sai dai ya kalubalanci Ganduje kan tilasta mashi yin gudun hijira.

Kara karanta wannan

Kano: Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku fahimta a hukuncin soke naɗin Sanusi II

"Dalilin kin zuwa na kotu" - Sanusi II

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa bai kalubalanci tsige shi da tsohon Gwamna Ganduje ya yi ba, Sanusi II ya ce:

"Na gaya muku cewa ba ni da wani hakki na zama sarki, ina daya daga cikin daruruwan 'ya'yan sarki, Allah ne ya zabe ni, kuma idan Allah ya ce in bar kujerar, zan dauki kaddara."
"Mu kaddara ma na je kotu, kuma ta ba ni nasara, kana tunanin zan ji dadin aiki da gwamnatin jihar? Tun da gwamnan ya nuna ba ya so na, ko da na dawo, zai kuntata rayuwata ne kawai.
"Kuma a kan me zan je kotu? Ko da aka kawo mun takardar kora daga sarauta, an ce ina yi wa gwamnati zagon kasa, amma ba su gabatar da hujja ba, kenan dai, tsana ce kawai ta jawo haka."

"Har yanzu Sanusi II ne sarki" - Dederi

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Yaron Sanusi II ya yi martani bayan hukuncin kotu kan dokar masarauta

Tun da fari, mun ruwaito gwamnatin jihar Kano, ta jaddada cewa har yanzu Muhammadu Sanusi II ne Sarkin Kano, duk da hukuncin da wata babbar kotu tarayya ta yi.

Kwamishinan shari’a na jihar, Haruna Isah Dederi ne ya bayyana hakan jim kadan bayan da kotu ta tabbatar da dokar rusa masarautun Kano amma ta rusa batun dawo da Sanusi II.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.