Sarautar Kano: Abba Kabir Ya Magantu Kan Mutuncin Aminu Ado, Ya Fadi Masu Zuga Shi

Sarautar Kano: Abba Kabir Ya Magantu Kan Mutuncin Aminu Ado, Ya Fadi Masu Zuga Shi

  • Gwamnatin jihar Kano ta yi magana kan yadda girman Aminu Ado Bayero yake a matsayinsa na mutum mai mutunci
  • Gwamnatin ta ce Aminu Ado dan jihar ne kuma mai mutunci wanda zai iya yawo duk inda yake so
  • Kakakin gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa shi ya bayyana haka inda ya ce wasu ke zuga Aminu Ado

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta ce rigimar sarautar da ake yi tsakanin Sanusi II da Aminu Ado fadar karshe ne.

Gwamnatin ta ce Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero yana da mutunci a jihar wanda ke da 'yanci a matsayinsa na dan kasa.

Kara karanta wannan

'Aminu Ado Bayero a makabarta yake zaune ba fadar Sarki ba' Inji Gwamnatin Abba

Gwamnatin Kano ta yi magana kan mutuncin Aminu Ado
Gwamnatin Kano ta bayyana yadda wasu ke zuga Aminu Ado Bayero. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Abba Kabir Yusuf, Masarautar Kano.
Asali: UGC

Abba Kabir ya fadi mutuncin Aminu Ado

Kakakin Gwamna Abba Kabir, Sanusi Bature Dawakin Tofa shi ya bayyana haka yayin hira da Arise TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bature ya ce bai dace Aminu Ado ya aikata abin da ya yi ba a matsayinsa na mutum mai mutunci, Daily Trust ta tattaro.

"Aminu Ado dan jihar Kano ne kuma mutum ne mai mutunci ba mu son wani abu ya faru da shi."
"Ba ya cikin wata takura domin barin jihar Kano, saboda girmansa a cikin al'umma, yana da damar yawo duk inda ya ke so."
"Rundunar 'yan sanda ta nuna bangaren da take yi kuma bata karbar umarni daga Gwamna Abba Kabir."

- Sanusi Bature

Kano: Yadda wasu ke zuga Aminu Ado

Bature ya ce tun farko Aminu Ado ya zo Kano da tsakar dare har ya kwashe kayansa amma wasu 'yan siyasa suka zuga shi ya dawo domin ya fafata.

Kara karanta wannan

"Na yafe muku", Bayan shan suka, Abba Hikima ya kare kansa kan sahihancin Aminu Ado

Ya ce a wurinsu wannan fadar karshe ne saboda gwamnan yana da damar tube sarki da kuma nada sabon sarki.

"Gwamnan ya nada ikon nadin sarki babu mai kwace hakan daga gare shi, saboda doka ta bashi dama."
Ko da zai kai shekaru 100 ne gwamnan yana da damar tube sarki ko kOrarsa tare da nada wanda yake so."

- Sanusi Bature

Abba Hikima ya magantu kan sahihin sarki

A wani labarin, kun ji cewa lauya Abba Hikima ya magantu kan sahihin sarkin Kano a yanzu yayin da ake dambarwa.

Lauya Hikima ya ce a mahangar doka a yanzu Aminu Ado Bayero shi ne sahihin Sarkin Kano mai cikakken iko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.