YANZU-YANZU: Ganduje ya kwancewa Sarkin Kano rawani
Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa gwamnatin jihar Kano ta tsige mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu.
Hadimin gwamnan Kanon kan sabbin kafafen yada labarai, Salihu Tanko Yakassai, ya bayyana hakan ne ranar Litinin, 9 ga watan Maris, 2020.
Yace: "Majalisar zartarwar jihar Kano ta amince da tsige sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II."
Hakazalika, sakataren gwamnatin jihar, Usman Alhaji, ya saki jawabi kan dalilin da yasa gwamnatin jihar ta tunbuke sarkin Kano daga kujerarsa.
Ya ce an kwancewa Sanusi Lamido Sanusi rawani ne saboda yan zubar da mutunci da kuma ko oho da dokokin masarautar.
Baya ga haka, Usman Alhaji ya ce Sarkin ya daina halartan dukkan ganawa da gwamnatin jihar ta shirya ba tare da wani uzuri kwakkwara ba kuma hakan rashin biyayya ne ga gwamnati.
Yace: "Ya kamata a sani cewa a lokuta da dama, Malam Muhammadu Sanusi II ya kasance mai karya sashe na 3 na dokar masarautar kuma idan aka cigaba da zuba masa ido, zai lalata mutuncin masarautar."
"An tunbukeshi ne bayan ganawa da masu ruwa da tsaki a jihar"
Mun kawo muku rahoton cewa Mambobin majalisar dokokin jihar Kano sun barke da fada da safen nan yayinda kwamitin binciken sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, ke shirin gabatar da rahoton kwance masa rawani. Daily Nigerian ta ruwaito.
Rikicin ya fara ne yayinda mataimakin kakakin majalisar, Hamisu Chidari, ya nemi izinin gabatar da rahoton yau.
Amma yan majalisar jam'iyyar adawa ta PDP suka ce a dakatad da gabatar da rahoton binciken sai ranar Talata domin kara dubi cikin rahoton; kawai sai rikici ya barke wanda ya kai ga dan majalisa mai wakiltar Warawa ya dauke sandar majalisa.
Masu idanuwan shaida sun bayyana cewa akwai alamun cewa yau za'a kwancewa sarki Sanusi rawani ko ta rahoton majalisar, ko kuma ta hukumar yaki da rashawar jihar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng