"Na Yafe Muku": Bayan Shan Suka, Abba Hikima Ya Kare Kansa Kan Sahihancin Aminu Ado

"Na Yafe Muku": Bayan Shan Suka, Abba Hikima Ya Kare Kansa Kan Sahihancin Aminu Ado

  • Bayan caccakar Abba Hikima kan fashin baki da ya yi a jiya Juma'a 21 ga watan Yunin 2024, lauyan ya magantu kan lamarin
  • Hikima ya ce ya yafewa wadanda suka yi ta zaginsa kan kalamansa game da dambarwar sarautar Kano da ake ciki
  • Lauyan ya kare kansa ne da wallafa wani hira da Farfesa Mamman Yusufari wanda ya tabbatar Aminu Ado Bayero ne Sarki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Fitaccen lauya a jihar Kano, Abba Hikima ya sha suka bayan tabbatar da Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano bisa doka..

Hikima ya yi fashin baki inda ya tabbatar da cewa babu wani matsala a shari'ar kamar yadda ake fada cewa akwai rudani.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Gingima-gingiman lauyoyi sun soki hukuncin kotu, sun zargi ƴan siyasa

Abba Hikima ya tabbatar da abin da ya fada kan sahihin Sarkin Kano
Abba Hikima ya wallafa hira da wani Farfesa da ke tabbatar da abin da ya fada. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Abba Hikima, Masarautar Kano.
Asali: Facebook

Kano: Abba Hikima ya kare kansa

Lauyan ya wallafa hira da aka yi da Farfesa Mamman Lawan Yusufari SAN wanda lauya ne a Facebook inda ya ke tabbatar da kalamansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, Hikima ya ce duk wadanda suka zage shi kan kalamansa ya yafe musu inda Farfesan ya tabbatar da fashin bakinsa.

Hikima ya yafewa wadanda suka zage shi

"Duk waɗanda suka zage mu jiya, na yafe amma ga Farfesa kuma SAN ya yadda 100% da abin da na fada a hirarsa ta yau."
"1. Ba matsala a dokar (a zahirin hukunci).
2. Nadin Sanusi bai yiwu ba a idon doka
3. Aminu ne Sarki."
"Daliban doka mu kyale masu zagi mu ci gaba da karatu."

- Abba Hikima

Fashin bakin da lauyan ya yi ya jawo masa zafi musamman daga wadanda ke goyon bayan Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II a jihar.

Kara karanta wannan

'Aminu Ado Bayero a makabarta yake zaune ba fadar Sarki ba' Inji Gwamnatin Abba

Abba Hikima ya fadi sahihin Sarkin Kano

Kun ji cewa fitaccen lauya a jihar Kano, Abba Hikima ya bayyana ainihin sahihin Sarki a yanzu bayan yanke hukunci.

Hikima ya ce babu wani rudani a cikin hukuncin kamar yadda ake yadawa inda ya ce komai a bayyane yake.

Lauyan ya ce a mahangar shari'a a yanzu Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero shi ne sahihin Sarki ba tantama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.