Sarautar Kano: Gingima Gingiman Lauyoyi Sun Soki Hukuncin Kotu, Sun Zargi Ƴan Siyasa

Sarautar Kano: Gingima Gingiman Lauyoyi Sun Soki Hukuncin Kotu, Sun Zargi Ƴan Siyasa

  • Wasu fitattun lauyoyi a Najeriya sun ki yin martani saboda zarge-zarge da ke cikin hukuncin kotu a sarautar Kano
  • Lauyoyin sun bayyana damuwa kan yadda aka yi hukuncin tare da saba wasu ka'idoji yayin shari'a a jihar
  • Sai dai wani daga cikin lauyoyin ya zargi yan siyasa da neman ruguza bangaren shari'a da kawo rigima a jihar Kano

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Yayin da ake ci gaba dambarwa kan sarautar Kano, wasu manyan lauyoyi sun ki cewa komai kan lamarin.

Daga cikin wadanda suka ki yin martani akwai Samuel Jibrin Okutepa SAN da Dakta Richard Oma Ahunauogho SAN da Israel Olorundare SAN.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu: Hadimin gwamna da fitaccen lauya sun samu saɓani kan hukuncin kotu

Fitattun lauyoyi sun yi martani kan rigimar sarautar Kano
Lauyoyi da dama sun ki cewa komai kan rigimar sarautar jihar Kano. Hoto: Masarautar Kano, Abba Kabir Yusuf.
Asali: Facebook

Kano: Lauya ya magantu kan rigimar sarauta

Mafi yawansu sun nuna damuwa kan yadda aka yi hukuncin cikin kura-kurai ba tare da kwarin takardun shari'a da za a yi duba kansu ba, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai wani fitaccen lauya da ya boye sunansa ya bayyana cewa akwai matsala wurin tabbatar da hukunci da aka yi.

Lauyan ya zargi ƴan siyasa da ƙirƙirar rikici a jihar domin biyan buƙatar kansu kamar yadda ya faru a Kudu maso Yamma a Jamhuriya ta farko.

Ya ce suna kokarin lalata bangaren shari'a saboda wasu manufofinsa marasa kyau a kasar shi ne musabbabin amfani da matsalar masarautun.

"Ina yawan bin abubuwan da ke faruwa kan rigimar Kano tun daga dokar sauke Aminu Ado da kuma dawo da Sanusi II."
"Na kuma bibiyi hukuncin da Mai Shari'a, Liman ya yi wanda ba shi da hurumin yin haka musamman abin da ya shafi masarautu."

Kara karanta wannan

"Ba a sauke Sanusi II ba," Gwamnatin Kano ta yi ƙarin haske kan hukuncun kotu

- Cewar lauyan

Kano: Lauyan ya koka kan bijirewa doka

Lauyan har ila yau, ya ce Kotun Koli ta taba yin hukunci a shari'ar tsohon gwamnan Gongola inda ta ce Babbar Kotun Tarayya ba ta da hurumin shiga lamarin shari'a.

Ya ce sai dai kuma idan za su tsallake wancan hukunci da aka yi a shekarar 1987 inda ya ce bai san inda Babbar kotun Tarayya ta samu hurumin yin haka ba.

Lauyoyin Arewa sun magantu kan sarautar Kano

Kun ji cewa kungiyar lauyoyin Arewacin Najeriya ta yabawa hukuncin kotu kan dawo da Aminu Ado Bayero.

Lauyoyin sun kuma tabbatar da cewa hukuncin shi ne abin da mutane da dama suke bukata a Kano na mayar da Aminu Ado.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.